Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Ministan Gidaje da Bunƙasa Birane, Arc. Muttaƙha Rabe Darma, ya nuna rashin jin daɗinsa kan jinkirin da ake samu wajen aiwatar da aikin gidajen shirin ‘Sabonta Fata’, wato ‘Renewed Hope Cities’ a Jihar Katsina, inda ya yi gargaɗin cewa, ’yan kwangilar aikin da suka gaza cika alƙawuran da ke cikin kwangilarsu na iya fuskantar hukunci.
Ministan ya bayyana haka ne yayin da yake duba yadda aikin ke gudana a wurin da ake aiwatar da shi. Ya soki wasu ’yan kwangila da suka kasa kammala ayyukan da aka ba su tun watan Disamban 2024, duk da cewa an ware musu wa’adin watanni shida kacal domin su gama.
A cewarsa, yayin da wasu ‘yan kwangila suka kammala ayyukansu cikin nasara, ciki har da aikin samar da wutar lantarki da kuma gina gidaje guda 128, wasu kuma sun kasa kammala ayyukan hanyoyi da gine-ginen gidaje duk da cewa fiye da shekara ɗaya da rabi kenan da aka ba su kwangilar.
“Ba daidai ba ne mutum ya rattaba hannu kan yarjejeniyar kwangila ya ce zai gama aiki cikin wani takamaiman lokaci, amma ya wuce fiye da sau uku na wa’adin da aka amince da shi ba tare da neman warin lokaci ba,” inji shi.
Ministan ya ce wasu ’yan kwangilar sun danganta jinkirin da ƙarancin kuɗaɗen gudanar da aiki, amma ya jaddada cewa hakan ba zai zama uzuri na karya yarjejeniyar kwangila ba. Ya bayyana cewa duk ɗan kwangilar da ya ga ba zai iya kammala aiki a kan lokaci ba, wajibi ne ya rubuta wa ma’aikatar neman ƙarin wa’adi. Sai dai ya ce babu wanda ya yi hakan, lamarin da ya nuna sun karya sharuddan yarjejeniyar da suka sanya hannu a kai.
Darma ya umarci jami’an Ma’aikatar Gidaje da Bunƙasa Birane ta Tarayya da su kira taro da dukkan ’yan kwangilar da ke aikin domin sanar da su rashin gamsuwar gwamnati da yadda aikin ke tafiya da kuma ingancinsa.
Haka kuma ya ba da umarnin a shirya cikakken rahoto da zai nuna matsayin kowace kwangila, ranar da aka bayar da ita, wa’adin da aka ƙayyade, kaso nawa aka kammala, da kuma sunayen kamfanonin da ke aiwatar da ayyukan.
“Ina son cikakken rahoto kan kowace kwangila da ke nan. Muna son sanin sunayen ’yan kwangilar, sharuɗɗan kwangilar, tsawon lokacin aiki da kuma kaso nawa aka kammala. Ina sa ran rahoton zai iso hannuna kafin ranar Talata ko Laraba,” inji shi.
Ministan ya kuma nuna damuwa kan alamun lalacewa da ya gani a wasu gine-ginen, yana mai cewa gwamnati ba za ta karɓi gidajen da ba su kai ƙa’ida ba.
“Idan muka karɓi waɗannan gidaje muka tarar suna da matsaloli ko lahani, ba za mu amince da su ba. Dole ne ’yan kwangilar su gyara duk wani kuskure kafin a karɓi aikin,” ya bayyana.
Duk da haka, Darma ya yaba da ingancin wasu gidajen da ya duba, yana mai cewa bai ga wata babbar tsaga ko matsalar gini a cikinsu ba.
“Daga abin da na gani, aikin gine-ginen yana da kyau. Amma ƙwararrun masu binciken gine-gine za su gudanar da cikakken bincike kafin gwamnati ta karɓe su,” inji shi.
Ministan ya bayyana cewa a halin yanzu Ma’aikatar Gidaje da Bunƙasa Birane ta Tarayya tana aiwatar da sama da gidaje 15,000 a faɗin ƙasar nan ta hanyoyi daban-daban na samar da kuɗi, ciki har da kuɗaɗen gwamnati kai tsaye, haɗin gwiwar gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu, da kuma tallafin Bankin Lamunin Gidaje na Tarayya (Federal Mortgage Bank of Nigeria) da Hukumar Gidaje ta Tarayya (Federal Housing Authority). Sai dai ya yi gargaɗin cewa bai kamata a dogara da rahotannin takarda kawai ba, yana mai cewa akwai banbanci tsakanin adadin gidajen da aka ce an kammala da abin da ya gani a zahiri. Ya ce, duk da cewa jami’ai sun ba shi rahoton cewa an kammala gidaje 250, binciken da ya gudanar ya nuna kusan gidaje 130 ne kawai suka kai matsayin kammalawa.
Ministan ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa ma’aikatar za ta ƙara himma domin ganin an kammala ayyukan gidajen tare da miƙa su ga waɗanda suka cancanta kafin ƙarshen wa’adin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
“Zan sadaukar da lokacina, ilimina, ƙoƙarina da ƙarfina domin tabbatar da an kammala waɗannan gidaje. Kafin ƙarshen wannan gwamnati, ina son ganin tsakanin kashi 80 zuwa 90 cikin 100 na waɗannan ayyuka sun kammala kuma an bai wa jama’a. Gidaje an gina su ne domin mutane, ba domin ɓeraye da dabbobi ba,” inji shi.
