Kasuwar hannayen jari ta ƙara Naira tiriliyan 131.66 a shekaru uku na mulkin Tinubu

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Kasuwar hannayen jari ta Nijeriya ta samu gagarumin ci gaba a cikin shekaru uku na gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, inda darajar kasuwar ta ƙaru da sama da Naira tiriliyan 131, lamarin da ya sanya wannan lokaci ya zama ɗaya daga cikin mafi nasara a tarihin kasuwar.

Bayanan da aka fitar sun nuna cewa darajar kamfanonin da aka jera a Kasuwar Musayar Hannayen Jari ta Nijeriya (NGɗ) ta tashi daga Naira tiriliyan 28.845 a watan Mayun 2023 zuwa Naira tiriliyan 160.509 a ranar 29 ga Mayun 2026.

Wannan na nufin kasuwar ta samu ƙarin Naira tiriliyan 131.664, wanda ya kai kashi 456.45 cikin ɗari na ci gaba cikin shekaru ukun farko na gwamnatin Tinubu.

Masana harkokin kuɗi sun danganta wannan nasara da sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnati ta aiwatar domin farfaɗo da tattalin arzikin ƙasa da kuma dawo da amincewar masu zuba jari.

Haka kuma, manyan kamfanonin bankuna, masana’antu da kayayyakin masarufi sun taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasar kasuwar, yayin da masu zuba jari suka nuna gamsuwa da manufofin da gwamnati ta aiwatar.

Bayanan NGɗ sun kuma nuna cewa Alamomin Gabaɗaya Na Kasuwa (All-Share Indeɗ – ASI) sun tashi daga maki 52,973.88 a ranar 28 ga Mayun 2023 zuwa maki 250,385.47 a ranar 29 ga Mayun 2026, wanda ke nuna ƙaruwa da kashi 372.66 cikin ɗari.

Masana sun bayyana cewa haɗakar gyare-gyaren tattalin arziki da sabbin dokoki ne suka taimaka wajen ƙarfafa kasuwar da kuma jawo hankalin masu zuba jari na cikin gida da na ƙasashen waje.

Daga cikin muhimman matakan da suka taimaka akwai cire tallafin man fetur da haɗa tsarin musayar kuɗaɗen ƙasashen waje a shekarar 2023, shirin sake ƙarfafa jarin bankuna da aka fara a 2024, da kuma amincewa da Dokar Zuba Jari da Harkokin Hannayen Jari ta 2025.

Babban Daraktan Kamfanin Sofuniɗ Investment and Communications, Mista Sola Oni, ya ce sauye-sauyen tattalin arzikin gwamnatin Tinubu sun taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa kasuwar hannayen jari.

A cewarsa, matakan da suka haɗa da cire tallafin mai, sassauta dokokin kasuwar canjin kuɗi, sake ƙarfafa jarin bankuna da kuma gyaran tsarin kuɗaɗen gwamnati sun ƙara wa masu zuba jari kwarin gwiwa.

Sai dai ya yi gargaɗin cewa duk da ribar da masu zuba jari suka samu, sauye-sauyen sun kuma jefa talakawa cikin ƙalubale na ɗan lokaci. Ya ce, hauhawar farashi, faɗuwar darajar Naira da tsadar rayuwa sun rage ƙarfin sayen kayayyaki na jama’a tare da matsa lamba kan kamfanonin da ke dogaro da kayayyakin da ake shigowa da su daga ƙasashen waje.

By ukarofi

Leave a Reply