Ina goyon bayan Tinubu ne don ba na fatan Nijeriya ta inganta – Keji Giwa

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Wani fitaccen attajirin ɗan kasuwa a Nijeriya, Keji Giwa, ya jawo cece-kuce a kafafen sada zumunta bayan wasu kalamai masu jan hankali da ya yi kan siyasa, kasuwanci da shugabanci a ƙasar.

A cikin wani bidiyo da ya bazu a shafukan sada zumunta, Giwa ya kare goyon bayan da yake bai wa Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, yana mai cewa siyasa na taka muhimmiyar rawa wajen nasarar kasuwanci a Nijeriya.

Attajirin, wanda ya yi fice a harkar gine-ginen gidaje da filaye, ya bayyana cewa duk ɗan kasuwar da bai fahimci alaƙar da ke tsakanin siyasa da ci gaban kasuwanci ba a Nijeriya, yana iya fuskantar matsaloli a harkokinsa.

Da yake mayar da martani ga masu sukar sa da ke kiransa mai cin amanar jama’a saboda goyon bayan Tinubu, Giwa ya ce bai ga dalilin da zai sa a riƙa sukar sa ba, yana mai cewa yin adawa da mai iko na iya jefa duk abin da ya gina cikin haɗari.

Ya ce, “Mutane da yawa suna fushi saboda ina goyon bayan Tinubu, suna kirana mai cin amana. Me suke so na yi? Su na son na shiga cikinsu na riƙa sukar mutumin da da umarni ɗaya zai iya rusa duk abin da na yi wa rayuwata?”

Giwa ya bayyana cewa babban abin da ya fi damunsa shi ne kare harkokinsa da kuma tabbatar da jin daɗin iyalansa, ba wai halin da ƙasar ke ciki ba.

Ya ƙara da cewa, ko Nijeriya ta samu ci gaba ko ba ta samu ba, shi kansa yana cikin yanayi mai kyau, har ma ya ce ba ya ganin matsala idan ƙasar ba ta inganta ba.

A cewarsa, “Ko Nijeriya ta inganta ko ba ta inganta ba, ni ina cikin walwala. A zahiri ma, ina sa ran kada ta inganta. Addu’arku daban take da tawa.”

Wani sashe na kalamansa da ya fi ɗaukar hankali shi ne lokacin da ya yi magana kan addini da makomarsa a lahira.

Attajirin ya ce, ya riga ya amince da yiwuwar shiga wuta idan har akwai ita, yana mai cewa akwai abubuwan da ya aikata da za su iya kai mutum ga irin wannan hukunci.

Ya kuma bayyana wata ƙa’ida mai tsauri da yake amfani da ita a kamfaninsa, inda ya ce duk ma’aikacin da ya yi kuskure sannan ya ce “Allah zai tanada”, zai kore shi daga aiki nan take.

A cewarsa, “A kamfanina, idan ma’aikaci ya yi kuskure sannan ya ce Allah zai tanada, nan take zan sallame shi daga aiki.”

Kalaman nasa sun haifar da muhawara mai zafi a kafafen sada zumunta, inda wasu suka soki ra’ayinsa, yayin da wasu kuma suka ce yana faɗar abin da wasu attajirai ke ɓoyewa a zukatansu.

Wasu masu sharhi sun bayyana kalaman a matsayin abin takaici da rashin tausayi ga halin da talakawan Nijeriya ke ciki, yayin da wasu ke ganin yana magana ne daga hangen nesa na ɗan kasuwa da ke ƙoƙarin kare muradunsa.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, Giwa bai sake yin wata ƙarin bayani ko janye kalaman nasa ba, yayin da muhawarar da suka haifar ke ci gaba da ɗaukar hankali a sassa daban-daban na ƙasar.

By ukarofi

Leave a Reply