Muna ƙoƙarin taimaka wa sanatocin da suka faɗi zaɓen fidda gwani su samu tikitin takara – Akpabio

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya bayyana cewa Majalisar Dattawa na kokarin ganin an samar da mafita ga wasu sanatocin da suka kasa samun tikitin tsayawa takara a zaɓukan fidda gwani domin babban zaɓen shekarar 2027.

Jaridar Blueprint Manhaja ta ruwaito cewa sama da sanatoci 40 daga jam’iyyun APC, PDP, NDC da sauran jam’iyyu sun rasa tikitin komawa takara bayan kammala zaɓukan fidda gwani.

Da yake jawabi bayan dawowar Majalisar Dattawa daga hutun makonni huɗu, Akpabio ya taya waɗanda suka samu tikitin takara murna, sannan ya nuna damuwa kan yawan sanatocin da suka kasa samun damar komawa takara.

“Ina taya musamman waɗanda suka samu amincewar jam’iyyunsu domin wakiltarsu a zaɓe mai zuwa murna. Na san siyasa tana tattare da nasara da rashin nasara, amma a sama da kowace nasarar mutum ɗaya akwai babbar nasara, wato nasarar dimokuraɗiyya,” in ji Akpabio.

Ya ƙara da cewa shugabancin Majalisar Dattawa ya yi mamakin yadda sanatoci masu ci da aka zaɓa suka yi asara a zaɓukan fid-da-gwani.

“A wannan Majalisar Dattawa mun yi alkawarin cewa za a samu ƙarancin waɗanda za su yi rashin nasara. Na san Shugaban Majalisa da sauran shugabanni suna aiki tukuru domin ganin an samu mafita. Saboda haka tun kafin lokaci ya yi, ina cewa taya mu duka murna, ba tare da la’akari da bambancin jam’iyya ba,” ya ce.

Daga cikin fitattun sanatocin da suka rasa tikitin komawa takara akwai Sanata Ned Nwoko, Sanata Gbenga Daniel, Sanata Danjuma Goje da kuma Sanata Rufai Hanga.

A wani bangare kuma, Akpabio ya nuna damuwarsa kan sace ɗalibai da malamai da aka yi a Jihar Oyo, yana mai tabbatar da cewa gwamnati na yin duk mai yiwuwa domin tabbatar da dawowarsu gida lafiya.

Ya bayyana lamarin a matsayin hari ga ɗan’adam baki ɗaya, tare da gargadin ‘yan siyasa da masu neman muƙamai da kada su yi amfani da irin waɗannan masifu domin neman farin jini na siyasa.

“A irin waɗannan lokuta akwai yiwuwar wasu su fara zargin juna ko neman ribar siyasa daga bala’i. Ya kamata ‘yan siyasa su guji irin wannan hali saboda neman suna mai arha,” in ji shi.

Akpabio ya kuma buƙaci ‘yan Nijeriya su ci gaba da mara wa jami’an tsaro baya wajen yaƙi da rashin tsaro, kare makarantu da al’ummomi, tare da tabbatar da cewa masu aikata laifukan ta’addanci sun fuskanci hukuncin da ya dace.

By ukarofi