Borno: Yadda annobar Kwalara ta kashe mutum 40, fiye da 3,000 ke asibiti

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Cutar Kwalara ta yi ajalin aƙalla muutm 40 a yayin da wasu sama da mutum 3,000 suke fama da ita a cikin wata guda a wasu kananan hukumomi bakwai a Jihar Bonor.

Manhaja ta ruwaito cewa al’ummomi 139 ne aka samu bullar cutar a kananan hukumomin Borno, Jere, Mafa, Konduga, Monguno, Ngala da Magumeri daga ranar 1 zuwa 28 ga watan Mayu, 2026.

A ranar Asabar, 30 ga watan Mayun ne dai Gwamnatin Jihar Borno ta sanar cewa cutar kwalara ta kashe mutum 37, a yayin da wasu 3,000 ke ci gaba da fama da ita.

Gwamnatinta sanar da haka ne, kwana uku  bayan ta fitar da rahoton bullar cututtuka da ke nuna cewa mutum 27 sun mutu, wasu 2,715  kuma sun kamu da cutar daga ranar 1 zuwa 27 ga watwan.

Sabbin alkaluman sun nuna an samu karuwar mace-mace 10 da sabbin wadanda suka kamu da mutum 285 cikin kwana uku kacal.

Gwamnatin Jihar ta bayyana damuwa game da saurin yaduwar cutar a garin Maiduguri, hedikwatar jihar, inda a nan aka samu fiye da rabin masu cutar.

Amma ’yan uwan marasa lafiyan da wakilinmu ya tattauna da su sun bayyana cewa yawan masu fama da cutar zai iya fin haka, suna masu bayyana cewa mutane da dama da suka kamu da cutar suna mutuwa a gida.

Wakilinmu ya zagaya yankunan da cutar ta fi kamari da asibitoci a Maidurugi da Jere, inda ya lura cewa cibiyoyin kula da lafiyar sun cika makil da majinyata.

A Babban Asibitin Brigediya Abba Kyari da ke Ngaranam, wakilinmu ya ga yadda ake jinyar marasa lafiya kimanin 10 a kan siminti sakamakon yawan majinyata.

Wakilinmu ya lura yawanin tantunan tamfol wadanda suke da matuƙar muhimmanci wajen killace marasa lafiya domin dakatar da yaɗuwar cutar, sun cika da mata da kananan yara.

Modu Sheriff, dan uwa ga wani mara lafiya, ya ce, dan uwan nasa “Ya yi amai sau biyu sannan ya fara gudawa. Mun kai shi kemis, amma nas ta ba da shawarar mu je cibiyar killacewa ta Nganaram. Yanzu yana nan ana jinyarsa.”

Wakilimu ya kuma ga ’yan uwa na marasa lafiya suna rike da ledan karin ruwan da ake wa ’yan uwansu, wadanda yawanci tsofaffin mata ne da kananan yara da suke kwance a kasa babu tabarma.

Ma’aikatan lafiya ga suna gudanar da matakan gaggawa ga marasa lafiya masu tsananin ciwo.

Wani ma’aikacin lafiya da bai so a bayyana sunansa ba ya ce, “Ba mu da ainihin alkaluman majinyata, amma akalla daga safiya zuwa wannan lokaci (12:30) mun karbi fiye da mtutum 40 a yau. Ga shi dai ka ga yadda cibiyar ta cika sosai.”

Ya ce barkewar cutar a bana ta yi tsanani idan aka yi la’akari da yawan marasa lafiya da aka samu zuwa yanzu.

“Kusan kananan hukumomi takwas na Borno an sabu bullar cutar kwalara, mafi yawan su kuma a nan Maiduguri da Jere ne,” inji shi.

Lokacin da aka tuntubi ofishin Kungiyar Likitoci ta Duniya (MSF) na Maiduguri, wanda ke aikin gaggawa a Cibiyar Maganin Kwalara, sun ki cewa komai, inda suka nemi wakilinmu ya rubuta takarda a hukumance ta imel kafin su ba da bayanai.

Lokacin da wakilinmu ya ziyarci yankunan da kwalara ta yi katutu a Shehuri Budum, Limanti, Shokari da Gamboru a cikin kananan hukumomin Maiduguri da Jere, mazauna yankin sun ce mutane da dama sun mutu kafin a kai su asibiti.

Wani wanda ya rasa mahaifiyarsa sakamakon kwalara a unguwar Shokari da ke gundumar Mashamari, Malam Abubakar Makah, ya ce cutar ta kashe mutane biyu kuma ta kama bakwai a yankin.

“Ta fara yin amai, sai gudawa ya biyo baya. Kafin mu yi wani abu, rai ya yi halinsa. Yayin da nake magana da kai, wani yaro ya mutu, kuma makwabtanmu guda shida sun riga sun kamu.

“Mun san abin da ya faru a nan shekaru da suka gabata; shi ya sa kowa yake tsoro. Muna rokon Allah kada irin wannan masifa ta sake faruwa. Mutane da yawa sun mutu,” inji shi.

Wani babban nas, Modu Ngudo, wanda yawanci ke ba da agajin farko a cikin al’umma kafin a kai marasa lafiya cibiyar jinya, ya koka cewa wasu daga cikin marasa lafiya ba sa zuwa asibiti.

“Na kan tilasta wasu su kai ’ya’yansu asibiti. An kawo min mutum shida. ɗaya daga cikinsu, tsohuwa ce. Abin takaic shi ne wasu har yanzu suna da tsoron zuwa asibiti. Akwai wani wanda ya kawo dansa wurina neman taimako. Na samu nasarar daidaita lafiyar rayon, sai na ce ya kai shi asibiti amma ya ki.

“Wani lokaci nakan yi barazanar cewa zan daina duba su; sai a lokacin suke yarda su kai ’yan uwansu CTC Nganaram,” inji shi.

Ya kuma bayyana cewa matsalar cutar ta fi muni a wuraren da mutane ke rayuwa cikin yanayi da ke taimaka wa yaɗuwar cutar.

“Akwai wuraren da al’umma ke dibo ruwa daga tafkin (Mother Cat Dam), da zarar ruwan ya gurbata, cutar za ta ci gaba da yaduwa,” inji shi.

Ya kuma ja hankali ka matsalar yin bahaya a fili matsayin wani abu da zai iya tayar da barkewar kwalara a wasu yankuna.

“Ko da gwamnati ta yi kokari wajen dakatar da yin bayan gida a fili, wasu za su ci gaba da yi, kuma yana shafar lafiyarmu,” inji shi.

Wani likita a asibiti, Tijjani Ammani, ya ce kwalara cuta ce mai tsanani ta gudawa da kwayar Vibrio cholerae ke haifarwa.

Ana gane ta da gudawa mai ruwa sosai, amai, da tsananin rashin ruwa a jiki, wanda zai iya bayyana da kishirwa mai tsanani, bushewar baki, ramewar idanun, raunin jiki, da ciwon tsoka. Idan ba a yi magani ba, yanayin na iya saurin rikidewa zuwa bugun jini da mutuwa.

Ya ce ana kamuwa da cutar ne musamman ta hanyar cin abinci ko shan ruwa da ya gurbata ko najasar wanda ya kamu ta ita.

Ya ƙara da cewa shan ruwan da ba a tace ba da cin abincin da aka dafa cikin yanayi mara tsafta na daga cikin manyan hanyoyin kamuwa.

Rashin tsafta, cunkoso, da rashin ingantaccen zubar da shara barkatai suna taimaka wa yaduwarta, inji shi.

Ammani ya kara da cewa rigakafin kwalara yana dogara ne da tsafta da tsare-tsaren lafiya.

“Shan ruwan da ya dace, wanke hannu akai-akai da sabulu, zubar da najasa yadda ya kamata, da dafa abinci sosai suna rage haɗarin kamuwa da cutar,” inji shi.

Gwamnatin jiha ta fitar da sanarwar lafiya a Maiduguri, tana gargadin mazauna su kiyaye tsaftar muhalli. Sakataren Zartarwa na Hukumar Lafiya ta Borno, Dakta Saleh Abba-Kaza, ya yi kira ga mazauna su ɗauki matakan kariya don dakile yaɗuwar cutar.

A cewarsa, an fara samun rahoton barkewar cutar ne a ranar 1 ga Mayu sannan aka tabbatar da ita a ranar 4 ga Mayu, tare da ci gaba da karuwa a cikin al’ummomin da abin ya shafa.

Ya ce, a ranar Asabar, fiye da sabbin masu cutar 100 aka samu cikin sa’o’i 24, yayin da Karamar Hukumar Binin Maiduguri (MMC) inda ke da masu cutar 2,000.

“ƙaramar Hukumar Jere ta samu mutum 1,000, yayin da Mafa, Konduga, Monguno, Ngala da Magumeri su ma abin ya shafe su,” inji shi.

Gwamnati ta kuma tura motocin asibiti da ma’aikatan jinya zuwa wurare tara a cikin babban birnin jiha domin daukar marasa lafiya cikin gaggawa.

Wuraren sun hada da: Mahadar Makabartar Gwange; Shehuri; Polo High Court; Flour Mill Junction; Kwanan Yobe; Mahadar Caji Ofis na Lamisula; Mashidimami daura da Bakasi Estate Junction da kuma Lawan Jidda.

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum, ya kuma umarci saye da rarraba magunguna da kayan jinya da kayan tsafta na miliyoyin Naira ga cibiyoyin lafiya a sassan jiha.

Sakataren Dindindin na Ma’aikatar, Dakta Shettima Maina Mohammed, ya bayyana hakan yayin gabatar da kayan jinya ga cibiyoyin lafiya da ke kula da marasa lafiya a ranar Lahadi.

A cewarsa, gwamnati ta sayi magunguna da kayan jinya sannan ta rarraba su zuwa cibiyoyin jinya da aka ware domin tabbatar da cewa marasa lafiya suna samun kulawa kyauta.

Sakataren dindindin ya yaba wa gwamna bisa sakin kuɗi cikin lokaci don sayen kayan jinya.

A matsayin wani bangare na kokarin dakile yaduwar cutar, tawagar da ta hada jami’an gwamnati da ma’aikatan lafiya ta gudanar da wayar da kai a cikin al’ummomin Maiduguri da Jere.

Tawagar ta ziyarci Shehun Borno, Alhaji Abubakar Ibn Umar Garbai El-Kanemi, domin neman goyon bayan masarautar wajen zaburar da al’umma da wayar da kai kan rigakafin cutar.

Dakta Mohammed ya yi kira ga shugabannin gargajiya da na al’umma su kara kokarin wayar da kan jama’a don karfafa mazauna su kiyaye tsafta da kuma neman kulawar likita da wuri idan alamun cutar suka bayyana.

Shehun Borno ya yaba wa Gwamna Zulum bisa matakin da ya ɗauka wajen shawo kan  arkewar cutar, tare da yin alkawarin goyon bayan masarautar wajen daƙile ta.

Tawagar ta kuma ziyarci al’ummomin Old Maiduguri, Gamboru, da Shehuri South, inda aka wayar da kan mazauna kan matakan kariya, ciki har da tsafta da kyakkyawan tsarin muhalli.

An kai magunguna, kayan jinya, kayan kariya da kayan tsafta iri-iri zuwa Asibitin Gaggawa da Cutar Kwayoyin cuta a Njimtilo da sansanin cutar Nganaram, inda ake kula da marasa lafiya a halin yanzu.

Haka kuma, a matsayin wani bangare na shirin, an rarraba kayan tsafta da ruwa (WASH), ciki har da kwayoyin chlorine, chlorine mai ruwa, magungunan kashe kwayoyin cuta, da kayan wayar da kan al’umma a wuraren da abin ya shafa don karfafa kariya da martani.

By ukarofi

Leave a Reply