DSS ta kama mutum biyar kan sace ɗalibai 300 a Neja

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Wasu mutane biyar da ake zargi da hannu a yin garkuwa da ɗalibai kimanin 300 a makarantar Katolika ta St. Mary Papiri da ke Jihar Neja, sun shiga hannu.

Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta bayyana cewa ta kama mutanen ne a yayin da suke safarar wasu bindigogi kirar ƙirar AK-47 guda 15 da harsasai 1,434 a cikin wata mota a kan hanyar Kaduna zuwa Zariya.

Daga cikin mutanen har da mutum biyu ’yan kasar Jamhuriyar Nijar da wani dan kungiyar Boko Haram da hukumar take nema mai suna Yusuf Mohammed wanda aka fi sani da Bature.

Bature, cewar hukumar, ya shiga hannun ne tare da abokinsa mai suna Mubarak Ibrahim a hanyarsu ta zuwa karbo wa kwamandojinsu makaman, daga bisani bayan bincike aka mako Goni Ibrahim, wani gawurtaccen mai safarar makamai na kasa da kasa daga yankin Diffa na kasar Jamhriyar Nijar.

Daga baya hukumar ta kara kama wani mai safarar makamai mai alaka da su mai suna Alhaji Adamu, wanda aka sani da Gado Banufe, wanda aka kama shi a yankin Yauri da ke Jihar Kebbi.

Majiyoyin tsaro sun ce binciken farko ya gano cewa mutanen da aka kama su ne suka samar da makamai ga ’yan bindigar da suka yi garkuwa da dalibai a Makarantar St. Mary da ke Papiri a watan Nuwambar 2025.

A rana 21 ga watan ne mahara a bisa baburua suka kutsa cikin makarantar kwanan, suka yi awon gaba da dalibai da malamansu.

Kimanin 50 daga cikin yaran sun tsere daga baya, ragowar kimanin 250 kuma aka tisa keyarsu zuwa cikin  jejin da ke Gandun Dajin Kainji.

A ranar 21 ga Disamba, 2025, Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Neja suka sanar da kubutar da yara 130 da malamansu, taer da jaddada cewa babu wanda ya rage a hannun masu garkuwa da su.

By ukarofi