Mahara sun kashe ’yan yawon sallah bakwai a Sakkwato

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Aƙalla mutum 17 ne, ciki har da masu yawon Sallah bakwai, suka rasa rayukansu bayan wani mummunan hari da ’yan bindiga suka kai ƙauyen Dangulbi da ke ƙaramar Hukumar Tureta ta Jihar Sakkwato.

Mazauna yankin sun shaida wa Aminiya cewa maharan, waɗanda suka zo kan babura kimanin 150 ɗauke da makamai, sun mamaye kauyen da safiyar Lahadi, inda suka riƙa harbe-harbe kan mai uwa da wabi tare da kwashe kayayyaki daga shaguna.

Wani mazaunin yankin da ya buƙaci a sakaya sunansa ya ce maharan sun shiga garin tsakanin ƙarfe 10 zuwa 11 na safe, kuma nan take suka fara harbi, lamarin da ya sa jama’a tserewa zuwa cikin daji domin tsira da rayukansu.

Ya ce daga cikin waɗanda aka kashe akwai baƙi bakwai da suka ziyarci ƙauyen domin yawon Sallah, biyar daga cikinsu sun fito ne daga ƙauyen Adarawa a ƙaramar Hukumar Gummi ta Jihar Zamfara, yayin da sauran biyun suka fito daga Gidan Gambo da ke ƙaramar Hukumar Shagari a Jihar Sakkwato.

Majiyar ta yi zargin cewa maharan sun fito ne daga yankin Bagega da ke ƙaramar Hukumar Anka a Jihar Zamfara, inda ta ce suka bi ta Barayar Zaki kafin su kwana a ƙauyen Gizazza sannan suka kai harin da safe.

A cewarsa, maharan sun shafe sa’o’i a cikin ƙauyen bayan harin, inda suka hana mazauna yankin fita domin gudanar da jana’izar mamatan.

“Sai bayan ƙarfe bakwai na yamma suka bar ƙauyen, sannan mutane suka dawo. Mun yi jana’izar mamatan ne da misalin ƙarfe 9:30 na dare,” in ji shi.

Rahotanni sun ce maharan sun kuma fasa tare da wawashe kayayyaki a shaguna kusan 20, lamarin da ya tilasta wa mutane da dama tserewa zuwa yankunan Gummi, Shagari, Tureta da Bukkuyum.

Bayan barin Dangulbi, an ce maharan sun kai hari wasu ƙauyuka da ke maƙwabtaka da yankin, ciki har da Kukoki da Birnin Magaji, inda suka yi garkuwa da wasu mutane.

Sai dai majiyar ta ce waɗanda aka sace sun samu damar tserewa ne bayan wata iska mai ƙarfi da ruwan sama da aka yi a daren Lahadi.

Mazauna yankin sun kuma yi zargin cewa maharan sun sake dawowa wasu ƙauyuka a safiyar Litinin, inda suka ci gaba da harbe-harbe da tada hankalin jama’a.

Sun yi kira ga gwamnatin tarayya da gwamnatin Jihar Sakkwato da su gaggauta kai ɗauki domin dakile hare-haren da suka ce suna ƙara ta’azzara a yankin.

Da aka tuntubi kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Sakkwato, ya tabbatar da cewa rundunar ta samu rahoton harin, yana mai cewa jami’an tsaro na ci gaba da aiki domin shawo kan lamarin.

By ukarofi