Gwamnatin Tarayya ta soke hutun wata uku kafin ritaya ga ma’aikatan gwamnati

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Gwamnatin Tarayya ta umarci dukkan Ma’aikatu, Hukumomi da Cibiyoyin Gwamnati (MDAs) da su daina aiwatar da tsarin da ake kira hutun watanni uku kafin ritaya ga ma’aikatan gwamnati, tana mai bayyana cewa babu irin wannan tanadi a cikin Dokokin Aikin Gwamnati (Public Service Rules).

Umarnin na kunshe ne cikin wata takarda da Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, Didi Walson-Jack, ta fitar zuwa ga ministoci, sakatarorin dindindin, shugabannin hukumomi da sauran manyan jami’an gwamnati.

A cikin takardar mai taken “Ingantacciyar Fassarar Dokar Aikin Gwamnati ta 120243 Kan Shirye-shiryen Ritaya”, Walson-Jack ta bayyana cewa wasu hukumomi sun yi kuskuren ɗaukar wa’adin sanarwar ritaya na watanni uku a matsayin hutun dole, lamarin da ke sa ma’aikata su daina aiki tun kafin lokacin ritayarsu ya cika.

Ta ce dokar ta tanadi abubuwa uku ne kacal ga ma’aikacin da ke shirin ritaya: bayar da sanarwar watanni uku kafin ritaya, halartar taron horaswa na wata guda kan rayuwar bayan aiki, da kuma kammala bayanan aiki da takardun fansho a cikin sauran watanni biyun.

“Abin da ake kira hutun watanni uku kafin ritaya ba shi da tushe a cikin Dokokin Aikin Gwamnati,” inji ta.

A cewarta, sanarwar watanni uku ba hutun aiki ba ne, illa dai wa’adin sanar da gwamnati cewa ma’aikacin zai yi ritaya.

“Ma’aikacin da ke shirin ritaya dole ne ya bayar da sanarwar watanni uku kafin ranar ritayarsa. Wannan sanarwa ce kawai, ba damar hutu ba,” in ji takardar.

Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayyar ta jaddada cewa ma’aikatan da ke dab da ritaya har yanzu ma’aikatan gwamnati ne kuma ana sa ran za su ci gaba da gudanar da ayyukansu yadda ya kamata har zuwa ranar ritayarsu, sai dai idan suna halartar taron horaswa ko kuma sun samu izinin hutu bisa ƙa’idojin aiki.

Ta ce dokar ba ta keɓe ma’aikatan da ke shirin ritaya daga gudanar da ayyukansu ba a lokacin sanarwar, sai dai idan suna cikin wani shiri na horaswa da aka amince da shi ko kuma suna kan wani hutu na hukuma.

Saboda haka, gwamnati ta umarci dukkan hukumomi da su daina tilasta wa ma’aikatan da ke dab da ritaya su bar ofis ko kuma su daina zuwa aiki kafin ranar ritayarsu ta hukuma.

Sabon tsarin ya tanadi cewa ma’aikatan da ke shirin ritaya za su ci gaba da gudanar da ayyukansu, su halarci shirye-shiryen horaswa da aka amince da su, sannan su kammala dukkan bayanan da suka shafi fansho da tarihin aikinsu kafin su bar aiki.

Haka kuma an umarci sakatarorin dindindin, daraktoci janar, shugabannin hukumomi da manyan jami’an gwamnati da su sanar da ma’aikata wannan sabon umarni tare da tabbatar da cikakken bin sa.

Ana sa ran wannan mataki zai shafi dubban ma’aikatan gwamnatin tarayya da ke ritaya a kowace shekara.

Tsawon shekaru, hukumomi da dama sun dauki wa’adin sanarwar ritaya a matsayin wani nau’in dogon hutu, inda ake hana ma’aikata ci gaba da zuwa aiki bayan sun gabatar da takardar sanarwar ritaya.

Gwamnati ta ce sabon umarnin zai taimaka wajen daidaita aiwatar da dokokin aikin gwamnati a dukkan hukumomi, tare da rage asarar ƙwararrun ma’aikata da ake samu sakamakon cire su daga aiki kafin lokacin ritayarsu.

Har ila yau, jami’an gwamnati sun bayyana cewa matakin zai taimaka wajen inganta ayyukan gwamnati, domin ma’aikatan da ke shirin ritaya za su ci gaba da bayar da gudunmawar iliminsu da ƙwarewarsu har zuwa ranar da za su bar aiki a hukumance.

By ukarofi