Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya sanar da sauya wa dukkan mataimakan gwamnan bankin guda huɗu wuraren aikinsu, a wani mataki da ke cikin sauye-sauyen da Gwamnan Babban Bankin Nijeriya, Olayemi Cardoso, ke aiwatarwa domin ƙarfafa sa ido kan harkokin kuɗi da inganta gudanar da manufofin tattalin arziki.
Sabon tsarin, wanda ya fara aiki daga ranar 1 ga Yunin 2026, ya haɗa da sake rabon jagorancin manyan sassan bankin da suka haɗa da sashen manufofin tattalin arziki, ayyuka, hidimomin gudanarwa da kuma sashen tabbatar da daidaiton tsarin kuɗi.
A wata sanarwa da bankin ya wallafa a shafinsa na intanet, an bayyana cewa an yi sauye-sauyen ne domin amfani da ƙwarewar manyan jami’ai a fannoni daban-daban tare da dacewa da sabbin manufofin ci gaban cibiyar.
A ƙarƙashin sabon tsarin, Dakta Muhammad Sani Abdullahi ya bar jagorancin Sashen Manufofin Tattalin Arziki inda aka mayar da shi shugaban Sashen Hidimomin Gudanarwa, wato Corporate Services Directorate.
Shi kuwa Philip Chukwuemeka Ikeazor ne zai karɓi ragamar Sashen Manufofin Tattalin Arziki, wanda ke da alhakin gudanar da binciken tattalin arziki da tsara manufofin da ke taimakawa wajen yanke shawarar kuɗaɗen ruwa, yaƙi da hauhawar farashi da sauran matakan kuɗi.
Haka kuma, Hajiya Emem Nnana Usoro ta bar Sashen Hidimomin Gudanarwa, inda aka mayar da ita shugabar Sashen Ayyuka (Operations Directorate), wanda ke kula da harkokin yau da kullum na bankin da kuma tafiyar da tsarin biyan kuɗi da kula da takardun kuɗi.
A gefe guda, Lamido Abubakar Yuguda ya koma jagorancin Sashen Tabbatar Da Daidaiton Tsarin Kuɗi, wato Financial System Stability Directorate, bayan ya bar Sashen Ayyuka.
Sashen Manufofin Tattalin Arziki na da muhimmiyar rawa wajen gudanar da bincike da tantance yanayin tattalin arziki domin taimakawa wajen tsara manufofin kuɗi na ƙasa.
Sashen Hidimomin Gudanarwa kuwa na kula da dukkan harkokin gudanarwa da tallafin cikin gida da ke tabbatar da cewa bankin yana gudanar da ayyukansa yadda ya kamata.
Sashen Ayyuka na kula da aiwatar da muhimman ayyukan banki na yau da kullum, yayin da Sashen Tabbatar Da Daidaiton Tsarin Kuɗi ke bibiyar haɗurran da ka iya tasowa a tsarin bankuna domin kare lafiyar harkokin kuɗi a ƙasa baki ɗaya.
Ko da yake CBN bai bayyana takamaiman dalilin sauya wa jami’an ayyukan ba, bankin ya ce irin wannan sauyi abu ne da aka saba yi a manyan cibiyoyi domin amfani da gogewar manyan jami’ai a fannoni daban-daban.
Sauye-sauyen na zuwa ne a lokacin da Babban Bankin Nijeriya ke ci gaba da aiwatar da gyare-gyare da nufin ƙarfafa amincewar jama’a da tsarin kuɗi, inganta sa ido kan cibiyoyin kuɗi da kuma tallafawa zaman lafiyar tattalin arzikin ƙasa.
Haka kuma, matakin ya zo daidai da ƙoƙarin da ake yi wajen aiwatar da shirin PSV 2028, wanda ke da nufin bunƙasa tattalin arzikin zamani da na fasahar dijital a Nijeriya.
