Cire harajin kashi 15 kan motocin tokunbo zai sauƙaƙa wa ’yan Nijeriya – Farinto

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Tsohon Muƙaddashin Shugaban ƙungiyar Dillalan Kwastom Masu Lasisi ta Nijeriya (ANLCA), Dakta Kayode Farinto, ya buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta soke harajin ƙarin kashi 15 da ake karɓa kan motocin da aka shigo da su daga ƙasashen waje (Tokunbo), yana mai cewa wannan tsari yana ƙara wa ’yan Nijeriya nauyin rayuwa a daidai lokacin da ake fama da matsin tattalin arziki.

Farinto ya bayyana hakan ne yayin da yake tsokaci kan tasirin sauye-sauyen tattalin arzikin da Gwamnatin Tarayya ke aiwatarwa.

Ya ce, duk da cewa manufofin gwamnati sun taimaka wajen ƙara kuɗaɗen shiga da kuma inganta wasu muhimman alamomin tattalin arziki, har yanzu talakawan Nijeriya ba su fara jin sauƙin da ake tsammani ba.

Ya amince cewa gwamnatin ta samu nasarori wajen daidaita kasuwar canjin kuɗaɗen waje da kuma ƙara kuɗaɗen da ake rabawa jihohi da ƙananan hukumomi daga Asusun Tarayya. A cewarsa, wannan na daga cikin lokutan da Nijeriya ta samu mafi yawan kuɗaɗen shiga a tarihin baya-bayan nan.

Sai dai ya jaddada cewa duk da irin waɗannan nasarori, rayuwar yawancin ’yan ƙasa ba ta inganta yadda ya kamata ba. Farinto ya ce sauye-sauyen tattalin arzikin suna aiki yadda ya kamata, amma har yanzu amfaninsu bai kai ga inganta rayuwar talakawa ba.

Ya kuma nuna damuwa cewa duk da ƙaruwar kuɗaɗen da jihohi da ƙananan hukumomi ke samu bayan gyare-gyaren tattalin arziki, ba a ga gagarumin ci gaba a fannin ababen more rayuwa da walwalar jama’a a matakin ƙasa ba.

Ya yi kira da a gaggauta cire harajin kashi 15 da ake ɗora wa motocin Tokunbo, yana mai cewa hakan zai rage wa masu shigo da motoci da masu saye wahala, musamman a lokacin da ake fama da hauhawar farashi, tsadar sufuri da kuma raguwar ƙarfin sayen jama’a.

Game da motocin lantarki, Farinto ya ce duk da matakan rangwamen haraji da gwamnati ta samar, matsalolin aiwatarwa sun hana shirin samar da gagarumin sauƙi a harkar sufuri.

A fannin tattalin arzikin ruwa kuwa, masanin harkokin jiragen ruwa ya buƙaci Ma’aikatar Harkokin Ruwa da Tattalin Arziki da ta ƙara himma wajen amfani da damar da hanyoyin ruwa ke da ita.

Ya ce, idan aka sarrafa wannan fanni yadda ya kamata ta hanyar haɗin gwiwar gwamnati da masu zaman kansu, za a iya samar da kuɗaɗen shiga har naira tiriliyan biyar a duk shekara. Ya kuma ba da shawarar saka hannun jari a harkokin sufurin ruwa da yawon buɗe ido, ciki har da ƙaddamar da jiragen yawon shakatawa na yankin Afirka ta Yamma domin samar da ayyukan yi da ƙara kuɗaɗen shiga.

Farinto ya yabawa Hukumar Kwastom ta Nijeriya kan sabon tsarin “One-Stop-Shop” da ta ƙaddamar, wanda ya rage yawan tsaiko da maimaita bincike kan kaya a tashoshin jiragen ruwa tare da ƙara saurin gudanar da ayyuka.

Haka kuma ya yaba da shirye-shiryen gwamnati na bunƙasa fitar da kayayyaki zuwa ƙasashen waje, yana mai cewa sun taimaka wajen ƙara yawan fitar da kaya, rage dogaro da dalar Amurka da kuma tallafa wa bunƙasar tattalin arziƙi. Ya kuma yi nuni da yarjejeniyar musayar kuɗaɗe tsakanin Nijeriya da Chana, yana mai cewa ta taimaka wajen ƙara ayyukan fitar da kayayyaki da kusan kashi 35 cikin ɗari.

A ɓangaren tsaro kuwa, Farinto ya nuna damuwa kan yadda matsalar rashin tsaro ke ƙara ta’azzara, yana danganta hakan da rashin cikakken haɗin kai tsakanin hukumomin tsaro wajen tattara bayanan sirri.

Ya buƙaci a ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin ’yan sanda, sojoji da sauran hukumomin tsaro, tare da kafa rundunar ’yan sandan jihohi domin ƙarfafa tsaro a matakin al’umma. Duk da suka da ya yi, Farinto ya ce tattalin arzikin Nijeriya na kan hanyar bunƙasa, inda ya bai wa gwamnatin tarayya maki kashi 55 cikin 100. Sai dai ya jaddada cewa dole ne a ƙara ƙoƙari domin jama’a su fara jin tasirin sauye-sauyen tattalin arzikin da ake aiwatarwa.

By ukarofi

Leave a Reply