Duk da haramcin NAFDAC, barasar leda ta ci gaba da mamaye kasuwanni

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Watanni bakwai bayan da Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta ƙasa (NAFDAC) ta fara aiwatar da haramcin sayar da barasar leda da kuma kwalaben roba masu ƙasa da mililita 200, har yanzu ana samun ci gaba da sayar da kayayyakin a cikin kasuwanni da kan tituna a sassa daban-daban na Nijeriya.

Binciken da wata jarida ta gudanar ya nuna cewa maimakon kayayyakin su ɓace daga kasuwa, har yanzu suna yawo a wurare da dama, yayin da kuma farashinsu ya yi tashin gwauron zabo tun bayan fara aiwatar da dokar.

A halin yanzu, barasar leda da a baya ake sayarwa kan kusan naira 100, yanzu tana kaiwa tsakanin naira 200 zuwa 250, gwargwadon wurin da ake sayar da ita. Haka kuma farashin giya cikin ƙananan kwalaben roba masu ƙasa da mililita 200 ya ƙaru matuƙa.

A kasuwar Tejuosho da ke ƙarƙashin gadar Yaba a Jihar Legas, wasu ‘yan kasuwa sun bayyana cewa duk da sun samu sanarwar shirin aiwatar da dokar daga NAFDAC, masu samar da kayayyakin sun zaɓi ƙara farashi ne kawai maimakon dakatar da rabonsu.

Wata mai sayar da kayan sha mai suna Obioma ta ce haramcin bai rage buƙatar kayayyakin ba a tsakanin masu amfani da su.

“Gaskiya ne mun samu sanarwa daga masu kawo mana kaya cewa NAFDAC za ta fara aiwatar da dokar, amma abin da kawai ya faru shi ne sun ƙara farashi,” inji ta.

Ta kuma nuna shakku kan tasirin dokar wajen rage shan barasa tsakanin yara da matasa, tana mai cewa da yawa daga cikinsu za su iya komawa sayen manyan kwalabe.

“Ko da an hana yara da matasa samun giya cikin leda, da yawa daga cikinsu za su iya komawa manyan kwalabe, wanda ma zai iya zama mafi haɗari saboda za su sha fiye da yadda suke yi a baya,” ta ƙara da cewa.

Tun farko dai ƙungiyoyin ma’aikatan masana’antar abinci da abin sha sun yi gargaɗi kan abin da suka kira gaggawar aiwatar da dokar, suna masu cewa hakan na iya jawo asarar ayyukan yi, ƙaruwa da safarar kaya ta haramtacciyar hanya da kuma raguwar kuɗaɗen shiga ga gwamnati.

By ukarofi

Leave a Reply