Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Bankunan ba da rance na bankunan ƙanana da matsakaitan sana’o’i (MFB) a Nijeriya sun samu gagarumar nasara a shekarar 2025, inda jimillar kuɗaɗen rancen da suka bayar ta ƙaru da kashi 92.8 cikin 100, daga Naira tiriliyan 2.30 zuwa Naira tiriliyan 4.43 a ƙarshen shekarar.
Sabbin alƙaluman da ke cikin Rahoton ƙididdiga na Babban Bankin Nieriya (CBN) sun nuna cewa ƙaruwar buƙatar rance daga ƙananan da matsakaitan ‘yan kasuwa, masu sana’o’in hannu da masu ƙaramin ƙarfi ta fuskar kuɗi ce ta haifar da wannan ci gaba.
Rahoton ya bayyana cewa adadin rancen da bankunan suka bayar ya tashi daga naira tiriliyan 2.30 a watan Janairun 2025 zuwa naira tiriliyan 4.43 a watan Disamba, abin da ke nuna yadda bankunan microfinance ke ƙara taka muhimmiyar rawa wajen samar da damar samun kuɗi ga al’ummar da ke fama da matsin tattalin arziki.
Alƙaluman sun nuna cewa rancen ya ƙaru daga naira tiriliyan 2.36 a watan Fabrairu zuwa tiriliyan 2.45 a watan Maris, sannan ya kai tiriliyan 2.68 a watan Afrilu da tiriliyan 2.95 a watan Mayu.
A watan Yuni, jimillar rancen ta haura matakin tiriliyan uku inda ta kai tiriliyan 3.12. Ci gaban ya bunƙasa a rabin na biyu na shekarar, inda adadin ya kai tiriliyan 3.33 a watan Yuli, tiriliyan 3.49 a watan Agusta da Satumba, kafin ya yi babban tsalle zuwa tiriliyan 4.14 a watan Oktoba. Daga nan ya ƙaru zuwa tiriliyan 4.39 a watan Nuwamba, sannan ya rufe shekarar da tiriliyan 4.43.
Masana harkokin kuɗi sun danganta wannan ci gaba da ƙarin buƙatar rance daga ƙananan da matsakaitan masana’antu (MSMEs), ‘yan kasuwa, masu sana’o’i da sauran mutanen da ke neman hanyoyin samun kuɗi saboda tsauraran sharuɗɗan rance da ake samu a bankunan kasuwanci.
Baya ga rance, bankunan microfinance sun kuma samu ƙarin amincewar jama’a, inda kuɗaɗen ajiyar da suka tara suka ƙaru da fiye da kashi 133 cikin 100.
Rahoton CBN ya nuna cewa kuɗaɗen ajiya sun tashi daga naira tiriliyan 2.15 a watan Janairu zuwa tiriliyan 5.01 a watan Disamban 2025. Adadin ya ƙaru daga tiriliyan 2.28 a Fabrairu zuwa tiriliyan 2.39 a Maris, sannan ya kai tiriliyan 2.47 a Afrilu.
A watan Mayu ya kai tiriliyan 2.76, yayin da ya ƙaru zuwa tiriliyan 2.79 a Yuni. A rabin na biyu na shekarar kuwa, ajiyar ta kai tiriliyan 3.12 a Yuli, sannan tiriliyan 3.29 a Agusta da Satumba. Babban ci gaba ya bayyana a watan Oktoba lokacin da adadin ya haura tiriliyan huɗu, inda ya kai tiriliyan 4.04, kafin ya ƙaru zuwa tiriliyan 4.14 a Nuwamba da kuma tiriliyan 5.01 a Disamba.
