Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Kotun ƙolin Nijeriya ta kawo ƙarshen taƙaddamar shari’a da ta dabaibaye haɗewar bankin Providus da Unity, bayan da ta yi watsi da ƙarar da aka shigar domin dakatar da haɗewar bankunan biyu, tare da umartar masu ƙarar su biya tarar Naira miliyan 10 ga kowanne daga cikin waɗanda ake ƙara.
Hukuncin ya fito ne daga wani kwamitin alaalai biyar na Kotun ƙoli ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Tijjani Abubakar, a ranar Litinin, inda kotun ta tabbatar da sahihancin haɗewar bankunan tare da kawo ƙarshen duk wata shari’a da ke da alaƙa da lamarin.
A cikin hukuncin da ake kallonsa a matsayin mai muhimmanci a tarihin harkokin banki a Nijeriya, Kotun ƙolin ta yi amfani da ikon da Sashe na 22 na Dokar Kotun ƙoli ya ba ta, inda ta amince kai tsaye da tsarin haɗewar bankunan biyu maimakon mayar da batun wata ƙaramar kotu domin ci gaba da sauraron sa.
Kotun ta umurci a miƙa dukkan kadarori, basussuka da sauran haƙƙoƙin Unity Bank, ciki har da filayen mallaka da gine-gine, zuwa hannun Providus Bank kamar yadda tsarin haɗewar ya tanada.
Haka kuma, kotun ta ba da umarnin kammala dukkan matakan canja wurin kadarorin cikin kwanaki goma daga ranar amincewa da haɗewar.
Dangane da tsarin biyan masu hannun jari, kotun ta amince da biyan naira 3.18 kan kowanne kaso na hannun jari, ko kuma ba masu hannun jari kaso 18 na Providus Bank na kobo 50 kowanne a madadin kaso 17 na Unity Bank da suke mallaka.
Baya ga haka, Kotun ƙolin ta ba da umarnin rushe Kwamitin Daraktocin Unity Bank ba tare da rufe bankin gaba ɗaya ba, sannan ta amince da sabon suna da za a riƙa amfani da shi, wato bankin ProvidusUnity.
Masu ƙarar, Suleiman Abubakar da Mohammed Goni Modu, waɗanda abokan hulɗa ne kuma masu hannun jari a bankunan, sun yi ta ƙalubalantar haɗewar tun daga Babbar Kotun Tarayya, suka wuce Kotun ɗaukaka ƙara kafin daga bisani lamarin ya isa Kotun ƙoli.
Da yake martani bayan hukuncin, babban lauya mai kare Unity Bank, Cif D.D. Dodo (SAN), ya bayyana hukuncin a matsayin tarihi da ya kawo ƙarshen duk wata jayayya kan haɗewar.
A cewarsa, hukuncin ya kawar da duk wata matsalar shari’a da ta rage a gaban aiwatar da haɗewar. Ya ce Kotun ƙolin ta fahimci muhimmancin haɗewar ga tattalin arzikin ƙasa, musamman wajen kare kuɗaɗen masu ajiya, tabbatar da dorewar ayyukan bankuna da kuma ƙarfafa tsarin kuɗi na ƙasar.
Dodo ya kuma bayyana cewa wannan na iya zama karo na farko a tarihin Nijeriya da Kotun Ƙoli ta amince kai tsaye da haɗewar bankuna ba tare da mayar da batun wata ƙaramar kotu ba.
Ya ƙara da cewa, hukuncin ya ƙarfafa manufofin Babban Bankin Nijeriya (CBN) na sake ƙarfafa jarin bankuna da bunƙasa tsarin haɗe-haɗe domin samar da manyan bankuna masu ƙarfi da za su iya tallafawa ci gaban tattalin arziki.
Haɗewar na daga cikin shirin ƙara jarin bankuna da Babban Bankin Nijeriya ya ƙaddamar, wanda ke ƙarfafa cibiyoyin kuɗi da ba za su iya cika sabon sharaɗin jarin banki ba su shiga haɗe-haɗe ko saye da haɗuwa da wasu bankuna.
Da wannan hukunci, an share fagen fara cikakken aiki da sabon bankin ProvidusUnity Bank Limited, wanda ake sa ran zai zama ɗaya daga cikin manyan bankunan da za su taka rawa a harkokin kuɗi da banki a Nijeriya.
