Mutane 60 a Kuwait sun jikkata yayin da Iran ta yi martanin harin Amurka

Spread the love

Sababbin hare-hare sun sake ɓarkewa a yankin Gulf ranar Laraba bayan harin da Iran ta kai ya lalata wasu sassan filin jirgin saman Kuwait tare da jikkata mutane fiye da 60.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito cewa an dakatar da zirga-zirgar jiragen sama na wani lokaci kafin daga baya a dawo da su bayan ɗaukar matakan tsaro.

Iran ta musanta kai harin kai tsaye filin jirgin, yayin da sojojin Amurka suka ce jiragen marasa matuƙi na Iran ne suka nufi wurin.

Rahoton ya ce sojojin Amurka sun kuma kai hare-haren kariya a kudancin Iran da kusa da mashigin Hormuz.

Duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma a baya, ɓangarorin na cigaba da musayar wuta a yankin na Gabas ta Tsakiya.

By Babaji