
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Jami’an Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) da haɗin-gwiwar jami’an ‘forest guards’, sun yi nasarar kama wasu magunguna da aka yi zargin an nufi kai wa mayaƙan ƙungiyar ISWAP ne a Jihar Borno.
Rahotanni sun bayyana cewa, al’amarin ya faru ne a ranar Juma’a yayin wani kimtsatstsen atisayen jami’an tsaro a Ƙaramar Hukumar Kaga, kamar yadda Zagazola Makama ya wallafa a kafar sada zumunta.
A rahoton nasa, Makama ya ce an gudanar da atisayen ne a wata hanya da ake zargin ana amfani da ita wajen yi wa ‘yan ta’adda safarar kayan aiki da kuma wasu yankunan dazukan jihar.
A cewar rahotan, ababen da aka ƙwato sun haɗa da magungunan ciwon jiki, alluran cutar zazzaɓin cizon sauro, masu yaƙi da ƙwayoyin cuta da wasu magungunan bature.
Haka kuma, ya yi zargin cewa an yi yunƙurin kai magungunan ne da nufin yi wa mayaƙan da suka jikkata a hare-haren da dakarun tsaron Nijeriya da na Amurka suka ƙaddamar magani.
Makama ya bayyana wannan nasara a matsayin ɓangare na kakkaɓe ayyukan ‘yan ta’adda ta hanyar dakatar da samar musu da magani da kayan aiki a maɓoyarsu daga jami’an tsaro.
Tuni dai aka garzaya da kayan zuwa ofishin hukumar tsaro domin gudanar da bincike akan su da kuma ƙoƙarin gano waɗanda ke da hannun acikin al’amarin da ɗaukar matakan doka akansu.
