Tinubu ya amince da kafa kwamitin shirin yaƙar cutar Ebola

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da kafa kwamitin na musamman kan shirin ƙariya daga cutar Ebola da sauran barazanar cututtuka masu yaɗuwa. Haka kuma ya amince da sakin Naira biliyan 10 domin ƙarfafa shirye-shiryen kariya da daƙile yiwuwar shigowar cutar Ebola cikin Nijeriya.

A cewar sanarwar da mai ba shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar, kwamitin zai kasance ƙarƙashin jagorancin Femi Gbajabiamila, tare da wakilan ma’aikatu, hukumomi da jihohi domin tsara matakan kariya da gaggawa kan lafiyar al’umma.

Matakin ya biyo bayan taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar domin nazarin yadda Najeriya ke shirin tunkarar yiwuwar ɓullar cutar, musamman bayan sake samun ɓarkewar Ebola a ƙasar Congo da Uganda. Taron ya samu halartar jami’an harkokin cikin gida, hukumar kula da filayen jiragen sama, shige da fice da sauran hukumomin da abin ya shafa.

Shugaba Tinubu ya kuma umarci dukkan jihohin da ke da filayen jiragen sama na ƙasa da ƙasa da kuma iyakokin ƙasa da su gabatar da shirinsu na kariya, buƙatun kuɗi da hanyoyin aiwatar da matakan da suka dace. Haka kuma an umurci hukumomi da su tsaurara binciken fasinjoji a filayen jiragen sama tare da ƙara sa ido kan jiragen da ke fitowa daga ƙasashen da ake ganin suna cikin haɗari.

Sauran matakan da aka amince da su sun haɗa da buɗe cibiyoyin killace masu zargin kamuwa da cutar a filayen jiragen saman Abuja da Legas, amfani da tsarin bayyana bayanan lafiya ta QR Code ga matafiya, da kuma tsaftace wuraren tashin jirage da kaya. Kwamitin zai kuma yi nazarin yiwuwar ware wasu tashoshi na musamman domin saukar jiragen da suka fito daga ƙasashen da ake sa ido a kansu domin tabbatar da cikakken bincike da kariya.

By ukarofi

Leave a Reply