
Majalisar Wakilai ta gayyaci manyan hafsoshin tsaro da Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara Akan Harkokin Tsaro (NSA), Malam Nuhu Ribaɗu, domin su bayyana a gabanta kan cigaba da taɓarɓarewar al’amuran tsaro a sassan ƙasar.
Matakin ya biyo bayan amincewa da wani ƙudirin gaggawa da ɗan majalisar mai wakiltar mazaɓar Gummi/Bukkuyum ta Jihar Zamfara, Hon. Sulaiman Abubakar Gumi, ya gabatar a zaman majalisar na ranar Talata.
Ɗan majalisar ya bayyana damuwarsa kan yadda hare-haren ‘yan bindiga, garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa da kashe-kashen fararen hula ke ci gaba da ƙaruwa a jihohi da dama, lamarin da ya ce yana barazana ga rayuka da dukiyoyin al’umma.
Bayan tattaunawa kan ƙudirin, Majalisar ta umarci Babban Hafsan Tsaron Ƙasa, Hafsan Sojin Ƙasa, Hafsan Sojin Ruwa, Hafsan Sojin Sama da kuma NSA su gurfana a gabanta domin yin cikakken bayani kan matakan da suke ɗauka wajen magance matsalar tsaro.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun rahotannin hare-hare, kashe-kashe da sacen mutane a jihohi da dama, musamman a yankunan Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya.
Majalisar ta bayyana cewa tana sa ran samun cikakken bayani daga shugabannin tsaron ƙasar kan matakan da ake ɗauka da kuma hanyoyin da za a bi wajen dawo da zaman lafiya da tsaron rayuka da dukiyoyin ‘yan Nijeriya.
