
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnatin Jihar Zamfara ta ƙaddamar da fayyacacciyar taswirar faɗaɗa Gusau, Babban Birninta da wasu birane a faɗin jihar.
Taswirar za ta bayar da damar faɗaɗa jihar na tsawon shekaru 20. Shirin ya ƙunshi samar da titina, ayyukan ci-gaban yawan al’umma, asibitoci, makarantu, ofisoshin gwamnati da cibiyoyin tsaro.
Kwamishinan Raya Gidaje da Birane na jihar, Ibrahim Nasiru Zurmi ne ya bayyana a haka a Gusau yayin hira da gidan rediyo Nijeriya.
Ya ce, tsarin aikin zai faɗaɗa daga Gusau zuwa Bunguɗu saboda kusancin iyakoki da kuma Ƙaramar Hukumar Tsafe.
Alhaji Ibrahim Zurmi ya bayyana cewa, bisa la’akari da samar da daidaito da adalci, an faɗaɗa aikin har zuwa ƙananan hukumomin Talata Mafara da Ƙaura Namoda, yana mai cewa gwamnatin jihar ta duƙufa wajen tabbatar da kowace ƙaramar hukuma ta amfana da ci-gaban.
A cewarsa, gwamnatin Zamfara tana yunƙurin warware dukkan matsalolin rikicin filaye da ƙarfafa lamuran harkokin ci-gaban birane a faɗin jihar.
Haka kuma, ya ce da dama daga cikin rikice-rikicen filayen sun samo asali ne daga saɓa wa tsarin taswira da gwamnati ta amince da shi da ya ƙunshi ma’aikata masu aiki da waɗanda suka yi ritaya, yana mai cewa gwamnatin ta ɗauki matakan daƙile yaɗuwar takardun filaye na bogi.
A ƙarshe, ya ce an samar da hanyoyin wayar da kan jama’a akan muhimmancin biyayya ga dokokin mallakar gine-gine a jihar domin kauce wa shiga rikicin fili ko gini.
