Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
Dan takarar Majalisar Wakilai ta Tarayya mai neman wakiltar ƙaramar Hukumar Bichi, Alhaji Saminu Shehu Amamu, ya bayyana cewa yana da kyawawan manufofi da tsare-tsaren ci gaba da zai aiwatar domin inganta rayuwar al’ummar yankin idan aka zaɓe shi a shekarar 2027.
Ya ce ya amsa kiran al’ummar Bichi ne domin ya tsaya takara tare da ba da gudunmawa wajen warware matsalolin da ke addabar yankin.
Saminu ya bayyana cewa ya fahimci bukatun jama’a kuma zai yi aiki tukuru wajen tabbatar da cewa an samu ci gaba mai dorewa a bangarorin ilimi, lafiya, samar da ayyukan yi da kuma inganta ababen more rayuwa.
Dan takarar ya ce ya zabi tsayawa takara a karkashin jam’iyyar NDC ne saboda manufofinta na kawo sauyi da kyautata rayuwar al’umma.
Ya kuma yabawa jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, bisa rawar da ya taka wajen bunkasa jam’iyyar NDC a Jihar Kano.
Saminu ya yi kira ga al’ummar jihar da su fito ranar zabe su kada kuri’unsu cikin hikima tare da marawa jam’iyyar NDC baya domin samun ci gaba da sauyi a Nijeriya.
