
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ƙungiyar Next Frontiers Nigeria (NFN) ta sanar da cewa ta samu halartar Taron Dabarun Inganta Al’umma na Ƙasa (NPSC), inda aka tattauna muhimman al’amura da suak shafi inganta lamuran tsaron Nijeriya da ciyar da harkokin ƙirƙira gaba acikn ‘yan Nijeriya.
An yi wa taron take da “Gina Tsarin Tsaron na Zamani a Nijeriya: Rawar Haɗin kan Hukumomin Tsaron Nijeriya a Kayayyakin Ƙasar”.
Amb. Kwamared Ɗahiru Muhammad Mai-Hula ne wakilin NFN a taron, a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin ƙungiyar wajen bayar da gudumawa a lamuran ci-gaban ƙasa, ƙirƙira da dabarun warware muhimman matsalolin ƙasa.
Da take jawabin, shahararriyar mai ayyukan jin-ƙai kuma wadda ta kafa ƙungiyar NFN, Dakta Fatima Usman Nazir ta jaddada muhimmancin kira ga amfani da kayayyakin gida.
Ta ce, taimaka wa masana’antun Nijeriya babban mataki ne na ci-gaban ƙasa musamman akan abin da ya shafi inganta matasan ‘yan kasuwa, masu ƙirƙira da mutane masu fasaha a ɓangarorin gwamnati da masu zaman kansu.
A cewarta, ƙarfafa ayyukan kayayyakin da ake samarwa a Nijeriya da kira ga siyansu za su taimaka wajen kai ƙasar yin gogayya da wasu ƙasashe, samar da damarmakin ayyukan yi da kuma faɗaɗa hanyoyin samun su a kasuwanni a ciki da wajen Nijeriya.
Mahalarta taron sun jaddada muhimmancin ƙarfafa tsarin tsaron Nijeriya a matsayin ginshiƙin tafiyar da harkokin masana’antu da ababen ƙirƙira cikin nasara da tsarin da ya dace da ƙasar, kamar yadda Amb Mai-Hula ya bayyana a sanarwar da ya fitar a ranar Lahadi.
Waɗanda suka samu halartar taron sun haɗa da Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Benjamin Okezie Kalu, CFR; Sanata Osita Izunaso; Ministan Tsaro, Janar Christopher Gwabin Musa (mai ritaya) da wasu jagororin masana’antu da kuma wasu manyan jami’an gwamnati.

