
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ranar Litinin Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta umarci da a soke rajistar jam’iyyar ADC da wasu jam’iyyu huɗu bisa gazawar cika sharuɗɗan dokar ƙasa akan jam’iyyun siyasa a Nijeriya.
Mai Shari’a Peter Lifu, wanda ya yi hukuncin, ya umarci Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC, da ta soke rajistar jam’iyyun tunda sun gaza samun kaso 25 na ƙuri’a a babban zaɓen da ya gabata domin biyayya da hukuncin doka.
Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa (NAN) ya ruwaito cewa, jam’iyyu biyar da suka haɗa ADC, Accord, AA, APP, da kuma ZLP ne kotun ta bayar da umarnin akansu.
Mai Shari’a Lifu ya yi watsi da dukkan ƙorafin da jam’iyyun suka yi akan al’amarin tare da umartar INEC da kada ta bar jam’iyyun su shiga zaɓuka masu zuwa ciki har da na 2027 saboda rashin cika ƙa’ida.
NAN ta ruwaito cewa, wata ƙungiya ta amitattun tsofaffin ‘yan majalisar dokokin ƙasa ne ta shigar da ƙara akan jam’iyyun a takarda mai lamba kamar haka: FHC/ABJ/CS/2637/2026.
Ƙungiyar ta ce jam’iyyun sun gaza cika sharuɗɗa da ƙa’idojin da dokar ƙasa ta tanada akan lamuran zaɓe da matakin ƙoƙari.
Akan haka ne ta nemi kotun da ta umarci a soke rajistarsu domin tabbatar da aiki da hukunce-hukuncen dokar ƙasa.
