Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe
Ƙungiyar Lauyoyin Najeriya (NBA), reshen Jihar Gombe, ta karrama tsohon babban alƙalin alƙalan Jihar Gombe, Mai Shari’a Mu’azu Abdulkadir Pindiga da lambar yabo ta ƙwarewa saboda gudummawar da ya bayar wajen bunƙasa harkokin shari’a da tabbatar da adalci.
An gabatar da lambar yabon ne a wani taro da ya samu halartar lauyoyi, alƙalai, jami’an gwamnati da sauran manyan baƙi a Gombe.
Shugaban NBA na reshen Gombe, Alhassan Mu’azu, ya ce an yi wa Mai Shari’a Pindiga wannan karramawa ne saboda jajircewarsa, gaskiyarsa da kuma irin rawar da ya taka wajen ƙarfafa tsarin shari’a a jihar.
Ya bayyana cewa tsohon babban alƙalin ya kasance abin koyi ga masu aikin shari’a, inda gudummawar da ya bayar ta taimaka wajen inganta harkar adalci da mutunta doka.
Da yake karɓar lambar yabon, Mai Shari’a Pindiga ya gode wa ƙungiyar bisa wannan karramawa, yana mai cewa hakan zai ƙara masa ƙwarin gwiwar ci gaba da tallafawa cigaban harkar shari’a.
Ya kuma yi kira ga lauyoyi da alƙalai da su ci gaba da aiki cikin ƙwarewa, gaskiya da riƙon amana domin ƙarfafa amincewar al’umma da tsarin shari’a.
Wasu daga cikin mahalarta taron sun yaba wa tsohon babban alƙalin, suna mai cewa gudummawar da ya bayar ga ɓangaren shari’a za ta ci gaba da kasancewa abin tunawa na tsawon lokaci.
