
Jam’iyyar adawa ta NDC, ta ƙara fayyace sabuwar dokar da ta ƙaddamar kan hana ‘yan takararta sauya sheƙa bayan sun ci zaɓe, inda ta tabbatar cewa ba za ta tilasta wa ɗan takarar shugaban ƙasa, Peter Obi, da mataimakinsa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, sanya hannu kan rantsuwar ba.
Tun farko dai jam’iyyar ta bayyana cewa duk mai neman takara a ƙarƙashinta dole ne ya sanya hannu kan yarjejeniyar kin sauya sheka, wadda za ta iya sa a ƙwace kujerar duk wanda ya fice daga jam’iyyar bayan samun nasara a zaɓe.
Sai dai a sabon bayani da Sakataren jam’iyyar na ƙasa, Ikenna Enekweizu, ya fitar, ya ce an yi gyara ga tsarin, inda aka cire manyan ‘yan takarar shugaban ƙasa daga wannan sharadi.
Ya bayyana cewa manufar dokar ita ce rage yawaitar sauya sheka da ake samu musamman daga ‘yan majalisun tarayya da na jihohi bayan sun lashe zaɓe a ƙarƙashin tutar jam’iyyar.
A cewarsa, jam’iyyar na son gina tsari mai ƙarfi da zai tabbatar da ladabtarwa, haɗin kai da kuma kare kuri’un da take samu a zaɓe.
Enekweizu ya ƙara da cewa matakin bai shafi shugaban ƙasa ko gwamnoni ba, sai dai ya fi karkata ga ‘yan majalisun da ake zaɓa a matakai daban-daban, domin hana su barin jam’iyyar bayan sun samu mukami.
Ya ce, “Manufar mu ita ce mu tabbatar da cewa jam’iyya na da ɗorewa, kuma duk wanda ya shiga ta san nauyin da ke kansa wajen mutunta dokoki da yarjejeniyoyi.”
Jam’iyyar ta ce wannan mataki na daga cikin gyare-gyaren da take yi domin ƙarfafa tsarinta gabanin zaɓukan 2027 da ke cigaba da ƙaratowa.
