
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Rundunar ‘Yan sanda a Jihar Kwara, ta kam wani da zargi da yi wa ‘yan bindiga safara kayan aiki a Ilorin, inda ta ƙwato wasu ababe da ake zargin yana kai wa ƙungiyoyin ta’addanci da ke ayyukasu a dazuka da wasu yankuna a jihar.
An yi nasarar haka ne bayan yaɗa wata jita-jitar kai harin ‘yan bindiga, lamarin da ya tilasta wa ɗaruruwan iyaye zuwa ɗauko ‘ya’yansu a makarantu.
A wata sanarwa da Kakakin rundunar, SP Adetoun Ejire-Adeyemi ya fitar a ranar Alhamis, ya ce sashen yaƙi da miyagun laifuka (VCRU) ne ya yi nasarar kamen bayan samun waɗansu bayanai na sirri da kuma amfani da salon ƙwarewar aiki.
A cewar ‘yan sandan, an gano cewa wanda ake zargi ya taka muhimmiyar rawa wajen samar da kayayyakin abinci da wasu nau’ukan taimako ga ‘yan bindiga da wasu masu aikata manyan laifuka.
Jami’an sun ƙwato nau’uka daban-daban na sigari da wasu ababe da ake zargin ana kai wa ‘yan ta’addar ne acikin dazukan da nufin ƙarfafa wa ayyukansu.
Masu bincike sun kuma samu wasu hotuna a wayar wanda ake zargin inda aka gan shi da shiga irin ta sojoji zaune akan babur ƙirar Bajaj, lamarin da ya ƙarfafa zargin jami’an akansa.
A cewar rundunar, ana cigaba da yunƙurin gano sauran mambobin tare da kama su domin su fuskanci hukuncin da dokar ƙasa ta tanada.

