A daina biye wa jita-jita, inji Ma’aikatar Kuɗi
Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta yi watsi da rahotannin da ke iƙirarin cewa, tana shirin ƙaƙaba sabbin haraji kan harkokin sadarwa da kayayyakin man fetur, bayan fitar da sabon rahoton tuntuɓar tattalin arziki na Asusun Lamuni na Duniya (IMF) kan Nijeriya.
Gwamnatin ta bayyana irin waɗannan rahotanni a matsayin kuskuren fassara abubuwan da ke cikin rahoton, tana mai jaddada cewa ba sa wakiltar manufofinta ko alƙiblarta ta fuskar tattalin arziki.
Ta kuma tabbatar wa da ’yan ƙasaR cewa, duk wani matakin haraji da za a ɗauka nan gaba za a sanar da shine ta hanyoyin hukuma tare da bin duk matakan doka da Kundin Tsarin Mulki.
A wata sanarwa da Shugaban Sashen Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na Ma’aikatar Kuɗi ta Tarayyar ƙasar, Mista Efe Ovuakporie, ya fitar, gwamnatin ta ce shawarwarin da ke cikin rahoton IMF ba wajibi ba ne ga Nijeriya, kuma bai kamata a ɗauke su a matsayin manufofin gwamnati ba.
Sanarwar ta ce, rahoton tuntubar tattalin arziki na Mataki na IV na IMF ya ƙunshi nazarin da asusun ya yi kan tattalin arzikin Nijeriya tare da bayar da shawarwari ga gwamnati, amma hakan ba yana nufin an amince da su ko za a aiwatar da su kai tsaye ba.
A cikin rahoton nata, IMF ta ba da shawarar matakan da za su taimaka wajen ƙara kuɗaɗen shiga ga gwamnati domin bunƙasa tattalin arziki da samar da kuɗaɗen gudanar da ayyukan raya ƙasa da tallafa wa jama’a. Daga cikin shawarwarin akwai yiwuwar ƙaƙaba haraji kan kayayyakin man fetur da kuma ayyukan sadarwa.
Sai dai gwamnatin tarayya ta ce duk wani hukunci da ya shafi haraji dole ne ya bi hanyoyin doka da na majalisa, tare da la’akari da bukatun ƙasa da yanayin tattalin arzikin da ake ciki.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa rangwamen harajin VAT da aka bai wa kayayyakin man fetur har yanzu yana nan daram, kuma ba a soke shi ba.
Hakazalika, gwamnatin ta ce duk da cewa wasu dokoki sun tanadi yiwuwar sanya ƙarin kuɗi kan man fetur, hakan ba zai fara aiki ba sai an fitar da umarnin minista tare da wallafa shi a Mujallar Gwamnati ta Hukuma, wato Official Gazette, abin da ta ce ba a shirin yi a halin yanzu.
Gwamnatin ta ƙara da cewa ci gaba da dakatar da irin waɗannan caje-caje ya taimaka wajen rage nauyin hauhawar farashin makamashi a duniya ga gidaje da ’yan kasuwa, tare da tabbatar da ɗan kwanciyar hankali a farashin man fetur a cikin ƙasa.
Dangane da ɓangaren sadarwa kuwa, gwamnatin ta bayyana cewa harajin da aka taɓa ƙaƙabawa kamfanonin sadarwa kafin shekarar 2023 an soke shi gaba ɗaya ƙarƙashin sabbin dokokin haraji da aka amince da su, saboda haka ba ya aiki a yanzu.
A ƙarshe, gwamnatin ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiwatar da gyare-gyaren tattalin arziki da za su ƙarfafa ci gaba, inganta tattara kuɗaɗen shiga, jawo masu zuba jari da samar da ayyukan yi, maimakon ƙara wa ’yan ƙasa nauyin haraji.
