Kotu ta ba da umarnin kama Sowore kan rashin halartar shari’a

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin kama ɗan gwagwarmaya kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar African Action Congress (AAC), Omoyele Sowore, bayan ya kasa halartar shari’arsa da ake yi kan zargin aikata laifukan yanar gizo.

Sowore na fuskantar tuhume-tuhume biyu da Hukumar Tsaro ta DSS ta shigar a kansa, bayan ya wallafa wani saƙo a shafukan sada zumunta inda ya kira Shugaba Bola Ahmed Tinubu da “mai laifi” (criminal).

A zaman kotun da aka ci gaba da yi ranar Talata, Sowore bai halarta ba, duk da cewa ya aika wa kotun wasiƙa yana bayyana cewa ya tafi Legas domin neman sabbin lauyoyin da za su kare shi bayan tsohuwar tawagarsa ta janye daga shari’ar.

Bayan sauraron buƙatar da DSS ta gabatar, Mai Shari’a Mohammed Umar ya soke belin da aka ba Sowore a baya tare da bayar da sammacin kama shi.

Tun da farko, Sowore ya zaɓi kare kansa a kotu bayan lauyoyinsa sun janye daga shari’ar. Ya kuma buƙaci Mai Shari’a Umar ya janye daga sauraron ƙarar, yana mai zarginsa da nuna son kai.

A cikin buƙatar da ya gabatar bisa tanade-tanaden Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na 1999 da aka yi wa kwaskwarima, Sowore ya yi nuni da wani lamari da ya ce kotun ta umarci lauyansa ya durƙusa a gabanta, wanda ya ce ya nuna rashin adalci.

Ya kuma bayyana cewa lauyoyinsa sun ƙi ci gaba da wakiltarsa saboda yadda kotun ta umurci a rika sauraron shari’ar a kullum da kuma abin da ya kira tsauraran matakan da kotun ke ɗauka.

“Lauyoyina sun gaya min cewa suna tsoron ci gaba da bayyana a gabanka saboda irin wulakancin da suka fuskanta a wannan kotu. Har sai na sami sabuwar tawagar lauyoyi, zan ci gaba da kare kaina,” inji Sowore a wata wasiƙa da ya gabatar.

An gurfanar da Sowore a gaban kotu a ranar 2 ga Disamba, 2025, kan tuhume-tuhumen da aka yi masa ƙarƙashin Dokar Hana Laifukan Yanar Gizo (Cybercrimes Act) ta shekarar 2024, inda ya musanta aikata laifin.

A cewar masu gabatar da ƙara, Sowore ya wallafa saƙonni a shafinsa na ɗ (Twitter) da Facebook a ranar 25 ga Agusta, 2025, bayan Shugaba Tinubu ya yi ikirarin a Brazil cewa gwamnatinsa ta kawo ƙarshen cin hanci da rashawa a Nijeriya.

ɗaya daga cikin saƙonnin da ake magana a kai ya ce: “Wannan mai laifi (@officialABAT) ya je Brazil yana cewa babu sauran cin hanci da rashawa a gwamnatinsa a Nijeriya. Wace irin ƙarfin hali ne na yin ƙarya ba tare da kunya ba?”

DSS ta ce saƙonnin na iya haddasa karya doka da oda tare da bata sunan shugaban ƙasa.

Hukumar ta kuma nemi kamfanonin ɗ da Meta su dakatar da asusun Sowore tare da cire saƙonnin, amma daga baya an cire sunayen kamfanonin daga cikin waɗanda ake tuhuma a cikin gyaran ƙarar da aka yi.

Yanzu haka ana sa ran jami’an tsaro za su aiwatar da umarnin kotu na kamo Sowore domin ci gaba da shari’ar.

By ukarofi

Leave a Reply