Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Sojojin Nijeriya sun bazama jihohin Katsina da Zamfara, don ci gaba da daƙile ayyukan ’yan bindiga, inda Rundunar Sojojin Sashe na Biyu a ƙarƙashin Operation Fansan Yamma ta sanar da ceto mutane bakwai da aka yi garkuwa da su tare da daƙile wani yunƙurin sace mutane da yin garkuwa da su a farmaki daban-daban da ta kai a yankunan jihohin.
A cewar rundunar, nasarar ta samu ne sakamakon ci gaba da gudanar da ayyukan yaƙi da ta’addanci, bincike da ceto domin murƙushe ayyukan ’yan ta’adda a yankin Arewa maso Yamma.
Cikin wata sanarwa da Jami’in Yaɗa Labarai na Rundunar Haɗin Gwiwa, Laftanar Kanar Aliyu Danja, ya fitar, ya bayyana cewa a ranar Litinin, 16 ga Yuni, sojoji sun gudanar da aikin ‘Operation Clean Sweep 3’ a yankin ƙaramar hukumar Matazu ta jihar Katsina.
Ya ce an ƙaddamar da aikin ne domin ƙara matsa lamba kan ‘yan ta’adda tare da tarwatsa hanyoyin sadarwarsu da kuma ceto mutanen da suka yi garkuwa da su.
A yayin aikin, sojojin sun kai farmaki kan wata maboyar ‘yan ta’adda da aka gano a ƙauyen Fafu da ke ƙaramar hukumar Matazu. Bayan musayar wuta mai zafi, ‘yan ta’addan sun tsere daga sansaninsu tare da ƙoƙarin guduwa da waɗanda suka sace.
Sai dai sojojin sun samu nasarar kwato sansanin tare da ceto mutane huɗu da aka yi garkuwa da su. An ce mutanen na samun kulawar lafiya saboda raunukan da suka samu yayin da suke hannun masu garkuwa da mutanen.
A wani samame makamancin wannan a jihar Zamfara, sojojin da ke aiki a yankin Zurmi sun dakile wani yunƙurin sace mutane bayan da wasu ‘yan ta’adda suka kai hari cikin wata al’umma da nufin yin garkuwa da mazauna yankin.
Da samun kiran gaggawa, sojojin sun garzaya wurin tare da fafatawa da ‘yan ta’addan, lamarin da ya tilasta musu tserewa zuwa cikin daji.
Bayan tabbatar da tsaron yankin, jami’an tsaron sun samu nasarar ceto wasu mutane uku da aka yi garkuwa da su tare da mayar da su ga iyalansu cikin ƙoshin lafiya.
Laftanar Kanar Danja ya ce saurin martanin da sojojin suka bayar ya hana ‘yan ta’addan cimma manufarsu ta sace jama’a a yankin da ke fama da matsalolin tsaro.
Ya ƙara da cewa nasarorin da aka samu sun nuna jajircewar rundunar Operation FANSAN YAMMA wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma a yankin Arewa maso Yamma.
“Sojoji za su ci gaba da kai farmaki kan maboyar ‘yan ta’adda domin hana su samun damar kai hare-hare ga jama’a tare da tabbatar da dawo da zaman lafiya a yankunan da abin ya shafa,” inji shi.
