Allah ba azzalumin kowa ba ne, inji Diezani bayan kotun Birtaniya ta wanke ta

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Tsohuwar Ministar Albarkatun Man Fetur ta Nijeriya, Diezani Alison-Madueke, ta bayyana cewa hukuncin da wata kotu a Birtaniya ta yanke na wanke ta daga zargin cin hanci ya kawo ƙarshen shekaru masu yawa na abin da ta kira “cin zarafi, suka da kuma tsangwama ba tare da adalci ba.”

Rahotanni sun nuna cewa Kotun Southwark Crown Court da ke birnin Landan ta wanke Alison-Madueke daga dukkan tuhume-tuhumen cin hanci guda shida da ake yi mata, bayan alƙalan shari’a sun shafe sa’o’i suna nazari kafin su yanke hukunci. Hakan ya kawo ƙarshen wata shari’a da ta ɗauki kusan shekaru 11 tana gudana.

Matsalolin shari’ar Diezani sun fara ne a watan Oktoban 2015 lokacin da aka kama ta a Landan, watanni kaɗan bayan ta bar muƙaminta a gwamnatin Nijeriya. Duk da cewa daga bisani an sake ta da beli, bincike kan zarge-zargen rashawa da cin hanci ya ci gaba tsawon shekaru.

A watan Agustan 2023 ne hukumomin Birtaniya suka gurfanar da ita a hukumance kan zargin karɓar cin hanci da ya kai fam dubu 100 na Birtaniya (yuro 100,000), yayin da aka fara sauraron shari’ar a watan Janairu na wannan shekara.

Masu gabatar da ƙara sun zargi tsohuwar ministar da karɓar kyaututtuka masu tsada da kuma anfani da gidaje na alfarma daga wasu manyan masu ruwa da tsaki a harkar mai da iskar gas, domin musayar ba su kwangilolin man fetur da iskar gas masu darajar miliyoyin fam.

Sai dai lauyoyin da ke kare ta sun shaida wa kotu cewa ikon Diezani wajen amincewa da irin waɗannan kwangiloli yana da iyaka, suna masu cewa yawancin muhimman shawarwari kan kwangilolin sun kan kammala tun kafin fayilolin su isa teburinta.

Da take mayar da martani cikin wani faifan bidiyo mai cike da tausayawa, Alison-Madueke ta gode wa Allah, iyalanta, abokanta da duk masu goyon bayanta da suka tsaya mata tsayin daka a tsawon wannan lokaci da ta bayyana a matsayin mai cike da wahala da kuma ƙunci.

“Na gode wa Allah. Kusan shekaru 11 kenan na gwagwarmaya mai wahala da kuma cike da damuwa. Ba ni kaɗai abin ya shafa ba, har da iyalaina, abokaina da duk waɗanda suka tsaya a bayana. Mahaifiyata mai shekaru 93 da ke Fatakwal, ɗana da sauran masoyana duk sun sha wahala tare da ni,” inji ta.

Ta ƙara da cewa: “Allah koyaushe yana aikata abin da Ya nufa. Allah ba mutum ba ne da zai yi ƙarya. Idan Ya yi maka alƙawari, tabbas zai cika shi.”

Tsohuwar ministar ta ce imaninta da dogaro ga Allah ne suka ba ta ƙarfin jurewa tsawon lokacin shari’ar.

“Na yi aikina gwargwadon iyawata. Amma kamar yadda na faɗa, Allah ba mutum ba ne da zai yi ƙarya. Allah shi ne Allah, kuma muna gode masa,” ta ƙara da cewa.

By ukarofi

Leave a Reply