An fitar da jaddawalin sabuwar kakar wasannin Premier ta Ingila

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Arsenal za ta fara kare kabenta na Premier League da ƙungiyar Coventry da ta samu damar dawo wa gasar a ranar 21 ga watan Agusta yayin fara sabon kakar wasa ta 2026/2027.

A ranar Juma’a ne aka fitar da jaddawalin wasannin gasar, inda Gunners za ta kara da Coventry na Frank Lampard a filin wasa na Emirates a birnin Landon.

Wannan shi ne karo na farko da Coventry ta samu shiga Premier League acikin shekaru 25 bayan ta lashe kofin Championship a kakar da ta gabata.

Ita kuwa Liverpool, za ta kara ne da Newcastle United a St James Park a ranar 23 ga Agusta.

Sai Manchester City da za ta fara gasa ba da koci Pep Guardiola ba a tsawon 10, inda za ta karɓi baƙuncin Bournemouth a ranar.

Sabon kocin Chelsea kuwa kuma tsohon ɗan wasan Liverpool, Xabi Alonso, zai fafata ne da Fulham a filin Craving Cottage a ranar 24.

Ita kuwa Manchester United, za ta ziyarci Hull City ne a gidanta a ranar 22 ga Agusta. Wannan shi ne karo na farko da Hull za ta buga wasan Premier League tun 2017.

A ranar 16 ga Agusta ne Arsenal da ta lashe gasar za ta kara da Man City da ta lashe kofunan Carabao da FA a wasan Community Shield.

Za a kammala gasar ne a ranar 30 ga watan Mayu, 2027, inda Arsenal za ranar karɓi baƙuncin Brighton, City za ta ziyarar Sunderland, sai kuma Bournemouth da za ta ziyarci Liverpool.

By Babaji

Leave a Reply