Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe
Tsohon babban mataimaki na musamman ga gwamnan Jihar Gombe, Barrista Aliyu Musa, ya fice daga jam’iyyar APC tare da ɗaruruwan magoya bayansa zuwa jam’iyyar PDP domin nuna goyon bayansa ga takarar gwamnan PDP tsohon ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Farfesa Isa Ali Pantami.
Aliyu Musa ya sanar da sauya sheƙarsa ne a ranar Asabar yayin wani taron siyasa da shirin Awareness and Unity Programme ya shirya a garin Billiri, hedikwatar ƙaramar hukumar Billiri ta Jihar Gombe.
A cewarsa, matakin da ya ɗauka ya samo asali ne daga yadda yake ganin Pantami a matsayin shugaba mai hangen nesa, ƙwarewa da gogewar da za su iya kawo ci gaba da bunƙasar tattalin arziki a jihar.
Ya ce Pantami ya nuna nagartaccen salon jagoranci a matakai daban-daban na rayuwarsa, lamarin da ya sa yake ganin ya cancanci samun goyon bayan al’ummar jihar.
Musa ya kuma yi kira ga al’ummar Billiri da sauran sassan jihar da su haɗa kai domin mara wa wannan buri baya, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen samar da shugabanci mai adalci da ci gaba mai ɗorewa.
A yayin taron, an kuma sanar da cewa sama da mambobi 1,800 na jam’iyyun APC da Labour Party (LP) daga ƙaramar hukumar Billiri sun sauya sheƙa zuwa PDP tare da bayyana goyon bayansu ga Pantami.
Shugabannin PDP na yankin sun yi maraba da sabbin mambobin, inda suka tabbatar musu da cewa za su samu cikakkiyar dama kamar sauran ’yan jam’iyyar wajen gudanar da harkokin siyasa.
Sun bayyana shigowar sabbin mambobin a matsayin wani babban ƙarfi da zai ƙara wa jam’iyyar tasiri a matakin ƙasa da tushe gabanin zaɓuɓɓukan siyasa masu zuwa.
Wasu daga cikin mahalarta taron sun ce yawan masu sauya sheƙar na nuna yadda goyon bayan Pantami ke ci gaba da ƙaruwa a sassa daban-daban na Jihar Gombe.
Taron ya samu halartar shugabannin jam’iyya, wakilan ƙungiyoyin matasa da mata, da kuma magoya baya daga gundumomi daban-daban na ƙaramar hukumar Billiri.
