APC ta lashe zaɓen cike gurbi na ɗan majalisar Kebbi mai wakiltar Zuru

Spread the love

Daga MUHAMMAD SADISU ABUBAKAR a Birnin Kebbi

Hukumar zaɓe ta ƙasa mai zaman kanta, INEC, ta ayyana ɗan takarar jam’iyyar APC, Garba Aiki Rabi’u a matsayin wanda ya ci zaɓen cike gurbi na shiga Majalisar Dokokin Jihar Kebbi mai wakiltar mazaɓar Zuru, da aka gudanar a ranar Asabar, 20/6/2026.

Jami’in bayyana sakamakon zaɓen, Farfesa Muhammad Bashar Danlami, na Jami’ar Gwamnatin Tarayya dake Birnin Kebbi, shi ne ya faɗi sakamakon zaɓen a Zuru a daren Asabar.

Farfesa Danlami ya sanar da cewar Garba Aiki Rabi’u na jam’iyyar APC ya samu ƙuri’a 4871 wanda ya doke abokin takararsa Aliyu Galadima Muhammad na jam’iyyar Labour Party, LP, wanda ya samu ƙuri’a 168.

Kwamishinan zaɓe na Jihar Kebbi, Alhaji Abubakar Dambo Sarkin Pawa, shi ya shugabanci zaman bayyana sakamakon zaɓen a Zuru.

Kafin gudanar da zaɓen na cike gurbi, kujerar ɗan majalisar ta zamo babu wanda ke a kan ta,sanadiyyar rasuwar tsohon shugaban majalisar dokokin Jihar Kebbi, Muhammad Usman Zuru, wanda shike wakiltar mazaɓar Zuru a majalisar.

By ukarofi

Leave a Reply