
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Rahotanni sun bayyana cewa mazauna a jihohin Kano, Katsina, Jigawa, Bauchi da Yobe za su fuskanci ɗaukewar wutar lantarki na wani ɗan lokaci a ranar Lahadi sakamakon aikin gyaran cibiyar rarraba wutar lantarki ta Kumbotso da Kamfanin Raba Wutar Lantarki na Ƙasa (TCN) ke yi.
A cewar rahotannin, an shirya aikin gyaran ne da nufin inganta tsarin samar da wutar lantarki a sassan jihohin.
Sannan, za a gudanar da aikin ne domin ƙarfafa tsarin isar da wutar lantarki da inganta hanyoyin samar da wuta a yankunan da abin ya shafa nan gaba.
Haka kuma, an bayyana cewa kamfanonin rarraba wutar lantarki za su fuskanci takaitaccen katsewar samar da wuta ga abokan huldarsu yayin gudanar da aikin.
Akan haka ne kamfanin ya buƙaci mazauna yankunan da abin ya shafa da su yi haƙuri tare da ɗaukar matakan da suka dace gabanin lokacin katsewar lantarkin.
