’Yan Nijeriya akwai ƙura fa

Spread the love

Daga ALI ABUBAKAR SADIQ

Makonnin da suka gabata na yi wani rubutu mai taken “Manakisar Amurka Ga Arewa”. Abubuwa biyu ne suka faru a wancan lokaci. Na farko shine sanarwar tsagaita wuta tsakanin Amurka da Iran. Na biyu kuma shine bayanin ƙasar Amurka na umarci ma’aikatan jakadanci da ’yan ƙasarta su bar Nijeriya da kuma nesantar jihohin Arewa.

Kamar yadda na bayyana a wancan rubutu cewa, tunda Iran ta gagari Amurka, inda ta kasa cimma muradunta da kuma datse mashigin Hormuz da Iran ta yi wanda ya janyo tashin gwauron zabi na farashin mai a duniya, yanzu Nijeriya ce a taswirar inda Amurkan ta dosa. Ajandar gwamnatin Trump ita ce ƙoƙarin mamaya da mallakar wani iko a ƙasashe uku masu mafi yawan mai a ƙarƙashin ƙasa da ke nahiyoyin Amurka ta Kudu (Venezuela) Gabas ta tsakiya (Iran) da Afirka (Nijeriya).

Sun riga sun mamaye Venezuela, sun gwada Iran abin bai kasance yadda su ka tsara ba. Yanzu hankalinsu ya karkato kan Nijeriya. Idan ba mu manta ba, wasu masu dattin ƙabilanci da bambancin addini aka yi amfani da su ba su sani ba, suka iza wutar maganar cewa, ana yi wa Kiristoci kisan ƙare-dangi a Arewa. Abin da ya bai wa Amurka ƙofar da take nema. A ranar kirsimeti su ka kawo hari Najeriya a Sokoto, ba yankin Kaduna (birnin gwari) ko Katsina da Zamfara ba inda ake da sansanonin Yan ta’addan daji da ke cin karensu babu babbaka ba. Sannan su ka turo sojoji yan leken asiri (kimanin 200) wadanda aka kai Bauchi (ba Katsina ko Zamfara ba). A cikin wadannan watanni wadannan sojojin na Amurka, na San cewa zuwa yanzu sun gama nazarin (mapping) Arewacin Najeriya gaba daya da reeper drones dinsu.

To, a jiya kuma sai ga Ted Cruz a wannan bidiyo na kasa inda ya bayyana a gaban kwamitin harkokin waje na majalisar dattawan Amurka, inda ya ke saka jaddada maganar kisan ƙare-dangi ga Kiristoci, har da bayanin cewa, a duniya babu inda ake kashe Kiristoci kamar Nijeriya domin an hallaka sama da 50,000 tare da ƙone majami’u da makarantu na kiristoci sama da 20,000.

Su Ted Cruz ɗin nan sune ’yan gaba-gaba wajen ingiza Trump ya biye wa Israila wajen far wa Iran farmaki. Iran ba irinmu ba ce, ta tashi ta kare kanta, saboda su na da shugabannin da al’ummarsu ce a gabansu.

’Yan siyasarmu babu abinda ke gabansu illa kawai ta yaya za su ci zabe, domin su ci gaba da wadaka da kudadenmu. Babu lokaci mai hadari a Najeriya irin lokacin da aka doso zabe da lokacin yin sa. Mu na barci da sakarci da tsanar juna da iza wutar kabilanci da bangarancin addini, a na can a na kokarin tarwatsa mu. Mu sani wallahi babu abinda mu ka fi Libya, Iraq, Sudan, Syria, Yemen…yau su na ina? Duk an tarwatsa su.

Tun bayan kifar da Ghaddafi Amurka ta Dana mana tarko da zaton za mu fada a 2015, har su ka bugi kirjin cewa Najeriya za ta tarwatse a 2015. Allah ya kwato mu, amma yan siyasa na dada nutsar da mu. Shin hasashen da Amurka ta gaza samarwa a 2015 shine ta ke son ya afku a 2027? To mu sani, sai mun bada dama hakansu zai cimma ruwa. Shin zamu tsaga wa kadangare bangon da zai sami shiga ne ko kuwa? Ku saurari wannan babban dillalin yaki ku ji abinda ya ke cewa, domin gano manufarsu a kanmu.

Ali mai sharhi kan harkokin yau da kullum ne

By ukarofi

Leave a Reply