Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa ta bayyana cewa aƙalla ‘yan Nijeriya 1,565,873 ne suka kammala rajistar katin zaɓe zuwa ranar 26 ga watan Yuni.
A cewar ƙididdigar da hukumar ta fitar a ranar Talata a Abuja, adadin ya kunshi mutum 620,933 da suka yi rajista ta yanar gizo, yayin da 944,940 suka kammala rajistar su a cibiyoyin rajista.
Sai dai INEC ta ce wannan kididdiga ta wucin gadi ce, domin za a sake tantance bayanan kafin a fitar da adadi na ƙarshe ta hanyar tsarin tantance bayanan masu rajista.
ƙididdigar ta nuna cewa Jihar Kano ce ta fi yawan sabbin masu rajista da mutum 118,207, sai Legas da mutum 78,360, sannan Delta da mutum 76,395.
Hukumar ta kuma bayyana cewa an dakatar da rajistar katin zaɓe na wani lokaci a jihohin Ekiti da Osun, sakamakon kammala zaɓen gwamnan Ekiti da kuma shirin gudanar da zaɓen gwamnan Osun, kamar yadda Sashe na 9(6) na Dokar Zaɓe ta 2022 ya tanada.
A ɓangaren sana’o’i kuwa, ɗalibai ne suka fi yawa da mutum 384,093, sai ‘yan kasuwa da mutum 333,539, sannan manoma da masu kamun kifi da mutum 273,627.
Rahoton ya kuma nuna cewa mutane 18,919 masu nakasa (PWDs) sun yi rajistar katin zabe a wannan lokaci.
INEC ta buƙaci dukkan ‘yan Nijeriya da suka cancanci yin rajista amma ba su yi ba da su shiga shafinta ko kuma su ziyarci cibiyoyin rajista na hukumar da ke faɗin ƙasar domin samun damar kaɗa ƙuri’a a zaɓuka masu zuwa.
