
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ƙasar Argentina ta samu tikitin zuwa zagayen ‘yan 16 a gasar Kofin Duniya bayan doke Cape Verde da ci 3 da 2 a wani wasa mai cike da armashi.
Duk da cewa Cape Verde ta yi rashin nasara, ƙungiyar ta nuna ƙwazo da jajircewa, inda ta tilasta wa fitacciyar ƙasar ta Kudancin Amurka yin aiki tuƙuru kafin ta tabbatar da nasarar.
Wasan ya kasance mai cike da hare-hare, inda Cape Verde ta cigaba da matsa lamba har zuwa mintunan ƙarshe, lamarin da ya sa Argentina ta sha wahala wajen kare jagorancinta.
Nasarar ta tabbatar da ci gaban Argentina zuwa zagayen ‘yan 16, inda za ta kara da Masar a wani wasa da ake sa ran zai kasance mai zafi da ɗaukar hankali.
Sai dai duk da ficewarta daga gasar, Cape Verde ta bar tarihi mai kyau a zukatan masu kallon ƙwallo saboda irin jarumtaka da ta nuna a karawarta da ɗaya daga cikin manyan ƙasashen duniya.
