Gwamnatin Tarayya za ta kafa kotun musamman domin saurin warware rikice-rikicen kasuwanci

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta bayyana shirinta na kafa Kotun Musamman ta Warware Rikice-rikicen Kasuwanci, domin hanzarta sasanta rikice-rikicen da suka shafi harkokin kasuwanci da zuba jari a faɗin ƙasar.

Ministan Kuɗi kuma Ministan Da Ke Kula da Harkokin Tattalin Arzikin ƙasa, Taiwo Oyedele, ne ya bayyana hakan a ranar Talata yayin da yake gabatar da lakcinsa na farko a matsayin ɗan ƙungiyar Masanan Ilimin Kasuwar Jari ta Nijeriya (CMAN) a taronta na biyu da ake gudanarwa duk bayan shekara biyu a Abuja.

Taron ya gudana ne ƙarƙashin taken “Kasuwar Jarin Nijeriya a Matsayin Ginshiƙin Ci Gaba Mai Adalci da Haɗin Kai.”

Oyedele ya ce, idan aka kafa wannan kotu kuma ta fara aiki, za ta taimaka wajen gaggauta yanke hukunci kan rikice-rikicen kasuwanci, lamarin da zai ƙara jawo masu zuba jari na dogon lokaci tare da bunƙasa kasuwar jarin Nijeriya. Ya bayyana cewa ɗaya daga cikin manyan matsalolin da ke hana masu zuba jari shigowa Nijeriya shi ne jinkirin warware shari’o’in kasuwanci, inda ya ce a halin yanzu ana iya ɗaukar kusan shekara 15 kafin shari’a ta bi ta Babbar Kotu, Kotun ɗaukaka ƙara da kuma Kotun ƙoli.

A cewarsa, sabuwar kotun za ta kasance ƙarƙashin alƙalai da masu sasanci da suka ƙware kan harkokin kasuwanci, kuɗi da kasuwar jari, tare da amfani da tsarin zamani na gudanar da shari’u ta hanyar fasaha da kuma wa’adin lokaci na dole wajen yanke hukunci.

Ya ce, wannan kotu za ta cike giɓin da ke akwai wajen kare masu zuba jari, domin za ta samar da hanya mai sauri ta warware saɓanin kasuwanci da ke jinkirta zuba jari tare da rage amincewar masu saka hannun jari.

Ministan ya kuma buƙaci ‘yan Nijeriya su sauya yadda suke kallon bashin gwamnati, yana mai cewa bai kamata a yi hukunci kan girman bashi kaɗai ba, sai an duba abin da aka kashe kuɗin da aka aro a kai.

Ya ce, abin da ya fi muhimmanci shi ne sanin dalilin karɓar bashin, farashinsa, ribar da ake sa ran samu da kuma yadda za a biya shi. A cewarsa, bashi ba matsala ba ne idan aka yi amfani da shi wajen aiwatar da ayyukan da za su samar da riba fiye da kuɗin ruwa da aka karɓa da shi. Oyedele ya kuma soki yadda wasu masu nazarin tattalin arziki ke sukar duk lokacin da gwamnati ta karɓi bashi ba tare da tantance ko an karkata kuɗin zuwa ayyukan ci gaba masu amfani ba.

Har ila yau, ya shawarci ‘yan kasuwa da kada su nace kan mallakar kaso 100 cikin 100 na ƙananan kamfanoninsu, yana mai cewa mallakar kaso mai tsoka a babban kamfani mai ƙarfi na iya fi samar da riba da ƙima. Oyedele ya gabatar da abin da ya kira “dokoki bakwai na jan hankalin jarin masu zuba jari,” inda ya ce masu saka hannun jari sun fi mayar da hankali kan amana, daidaiton manufofin gwamnati, ƙarfafan hukumomi da kuma bin doka, fiye da rangwamen haraji.

Ya ce, rashin tabbas a manufofi, sauya dokoki akai-akai, rashin tabbas kan musayar kuɗaɗen waje da kuma rashin tabbatar da aiwatar da kwangila na daga cikin abubuwan da ke tsoratar da masu zuba jari.

By ukarofi

Leave a Reply