
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnatin Venezuela ta ce adadin mutanen da aka tabbatar mutuwarsu sakamakon munanan girgizar ƙasa guda biyu da suka auku a ƙarshen watan da ya gabata a kasar ya kai 3,000.
Rahotanni sun bayyana cewa, har yanzu ana cigaba da bincike domin gano sama da mutum 40,000 da ba a san inda suke ba.
Haka kuma, masu aikin ceton gaggawa a arewacin Venezuela na cigaba da aikin zaƙulo gawarwaki daga ƙarƙashin baraguzan gine-ginen da suka rushe a sanadiyyar faruwar al’amarin.
Shugaban majalisar dokokin ƙasar, Jorge Rodriguez, wanda kuma ɗan uwa ne ga shugabar riƙon ƙwarya ƙasar ne ya bayyana cewa ana cigaba da gudanar da ayyukan ceto a yankunan da iftila’in ya shafa.
