Matasa ‘yan ƙwallo daga Katsina sun lashe gasar IberCup Estoril a ƙasar Portugal

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a katsina

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya taya ’yan wasan ƙungiyar koyar da ƙwallon ƙafa ta Katsina Football Academy murnar lashe gasar ƙwallon ƙafa ta IberCup Estoril 2026 da aka gudanar a birnin Lisbon, ƙasar Portugal.

Ƙungiyar, wacce ta wakilci Katsina ta hanyar haɗin gwiwa da Moonluck Football Academy, ta lashe kofin ne bayan doke GD AMB Football Club a wasan ƙarshe da aka buga.

A yayin gasar, matasan sun nuna ƙwarewa inda suka doke wata ƙungiya daga Guinea-Bissau da ci 1-0, sakamakon ƙwallon da ɗaya daga cikin yan wasan da Katsina, Sadiq Salihu ya zura.

Gwamna Raɗɗa ya bayyana nasarar a matsayin abin alfahari ga Katsina da Najeriya gaba ɗaya, yana mai cewa ta nuna irin hazaƙa da damar da matasan jihar ke da ita a fagen ƙwallon ƙafa.

By ukarofi

Leave a Reply