Masarautar Gobir na ɗaya daga cikin tsofaffin daulolin ƙasar Hausa, kuma tana daga cikin manyan masarautun da suka taka muhimmiyar rawa a tarihin Arewacin Nijeriya da yankin Sahel.
A tarihin da aka fi sani, ƙasar Gobir ta yi iyaka da Agades daga arewa, Zamfara daga kudu, Mayali daga gabas, sannan daga yamma ta yi iyaka da Konni.
Sai dai, akwai ra’ayoyi mabambanta kan asalin Gobirawa. Wasu masana da masu riƙe da tarihin gargajiya na cewa Gobirawa ba Hausawa ba ne a asali, suna kuma danganta asalinsu da Gabas ta Tsakiya, musamman ƙwasar Masar (Egypt). Haka kuma, akwai masu cewa wasu daga cikin sarakunan tsohuwar Misira sun kasance Gobirawa, duk da cewa masana tarihi ba su cimma matsaya guda kan wannan ikirari ba.
A wata hira da jaridar Daily Trust ta yi da Sarkin Gobir, Mai Martaba Alhaji Abdulhamid Balarabe Salihu, ya bayyana cewa a cewar tarihin gargajiyar masarautar, Gobirawa sun fito ne daga Misira, kuma su jikokin Annabi Nuhu (A.S.) ne. Ya ce sun bar Misira ne sakamakon tsananin zaluncin sarakunan zamaninsu, sannan suka isa wani wuri mai suna Gubur, inda daga sunan wurin ne aka samo sunan Gobir.
Sarkin ya ƙara da cewa daga Gubur suka nufi ƙasar Yemen, inda suka shahara wajen yaƙe-yaƙe saboda jarumta da ƙwarewar yaƙi. Daga nan suka wuce zuwa Libya, sannan suka isa yankin Azbin, wanda a yau ya kasance cikin yankunan da al’ummar Tuareg ke zaune.
Bayan sun bar Azbin, suka ratsa Hamadar Sahara har suka kafa wani gari mai suna Magali, daga bisani kuma suka koma Surukul. Dukkan waɗannan wurare na cikin Jamhuriyar Nijar ta yanzu.
Daga nan ne Gobirawa suka ci gaba da matsowa har suka isa Birnin Lalle da Gwararramu tsakanin ƙarni na 15 da na 16.
A wancan lokaci, Sarkin Zamfara Abarshi ne ke mulki daga garin Katanga. An ce ya auri Fara, ‘yar Sarkin Gobir, wadda daga baya ta haifi Ibrahim Babari.
A cewar tarihin gargajiya, kafin Ibrahim Babari ya zama Sarkin Gobir, ya taɓa fafatawa da Sarkin Zamfara kuma ya yi galaba a kansa. Wannan ya sa Sarkin Zamfara ya ƙuduri aniyar kashe shi. Sai dai, mahaifiyarsa ta mayar da shi ƙasar Gobir, inda daga baya ya hau gadon sarauta ta ɓangaren mahaifiyarsa.
An ce Ibrahim Babari ya nemi a ba shi yankin da zai zauna a cikin ƙasar Zamfara. Sai dai wasu sun gargaɗi Sarkin Zamfara cewa idan ya amince da hakan, wata rana Gobirawa za su mamaye ƙasar. A cewar wannan tarihi, abin da aka yi hasashe shi ne ya faru daga baya, lokacin da yaƙe-yaƙe suka ɓarke tsakanin ƙarni na 16 da na 17, inda Gobirawa suka mamaye yankuna da dama, ciki har da Alƙalawa, wanda daga baya ta zama babban birnin Masarautar Gobir.
Sarkin Gobir ya kuma yi magana kan shahararren Sarkin Gobir Bawa Jan Gwarzo, wanda ya yi mulki a ƙarni na 17. Ya ce an ruwaito cewa ƙarfin ikonsa da tasirinsa ya kai matsayin da ake cewa “ko zakaru ba sa cara” a zamaninsa. Haka kuma, Gobirawa sun shahara da jarumta, kuma a yaƙe-yaƙensu ba sa miƙa wuya ga abokan gaba. Wannan ne ya sa ake yi musu kirari da: “Gobir gidan faɗa.”
Dangane da alaƙar Shehu Usmanu ɗanfodiyo da Sarkin Gobir Bawa Jan Gwarzo, Sarkin Gobir ya ce Bawa bai taɓa yaƙi da Shehu ba. A cewarsa, Shehu Usmanu ɗanfodiyo ma ya kasance malamin ‘ya’yan Bawa Jan Gwarzo, ciki har da Yunfa, Atiku, Bello da Mayaki. Ya ce Shehun ya kan yi musu nasiha da su guji samun rarrabuwar kawuna a tsakaninsu.
Sai dai Sarkin ya ce wasu daga cikin mutanen da ke kusa da Bawa Jan Gwarzo ne suka haddasa saɓani tsakanin Shehu da masarautar Gobir, abin da ya sa Shehu ya bar Alƙalawa, daga bisani kuma ya ci gaba da yaɗa jihadinsa a yankin Sakkwato.
Game da tsagar Gobirawa, Sarkin ya bayyana cewa a asali ba su da wata tsaga ta musamman a fuska. Amma saboda yawan ƙaura da tafiye-tafiye sakamakon yaƙe-yaƙe, sai suka ƙirƙiri tsarin tsaga domin su riƙa gane junansu a duk inda suka haɗu
