Borno: Harin Boko Haram tsakar dare ya yi ajalin amarya da wasu biyu a sansanonin sojoji

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Wasu da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne sun ƙaddamar da hare-hare a sansanonin sojoji guda biyu da ke Maiduguri a Jihar Borno, lamarin da ya yi ajalin mutane uku.

Rahotanni sun bayyana cewa, maharan sun kai farmakin ne da misalin ƙarfe 2:14 na daren wayewar Juma’a a sansanin Kofa, kana daga nan suka zarce zuwa wani wajen sojoji a yankin Muna da ƙarfe 2:30.

Shaidu da mazauna yankunan da al’amarin ya shafa sun ce maharan sun kutsa ne akan babura, inda suka riƙa harbe-harbe na kan-mai-uwa da wabi, lamarin da ya rikita jama’a suka shiga halin neman tsira.

Majiyoyi sun bayyana cewa, dakarun tsaro sun yi nasara daƙile hare-haren, saida fararen hula uku sun rasu a lokacin da ake ba-takashi da mayaƙan.

Wata mazauniyar Kofa mai suna Deborah Usman ta bayyana cewa da dama daga cikin ‘yan yankin sun riƙa tsere wa rayukansu yayin da ake musayar wuta tsakanin sojoji da maharan.

A cewarta, ɗaya daga cikin waɗanda rasa rayukansu matara aure ce da aka auro makonni uku da suka gabata.

Haka ma, ‘yan yankin Muna sun ce mayaƙan sun farmaki sojojin da aka jibge ne a ofishin Kwastom, a wani yunƙuri na karya lagon jami’an tsaron da ke ba Maiduguri kariya.

Kazalika, wani mai suna Munnanaye Muhammad, wanda ɗan Muna ne, ya ce mutane biyu sun rasu yayin da suke ƙoƙarin tsere wa farmakin.

By Babaji

Leave a Reply