ICPC ta gurfanar da tsohon minista, Uche Nnaji

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A yau Litinin Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) ta gurfanar da tsohon Ministan Ƙirƙira, Kimiyya da Fasaha, Uche Nnaji a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja bisa zarge-zargen da suka shafi amfani da takardun karatu na bogi da karkatar da akalar kuɗaɗen al’umma.

A cewar hukumar, tuhume-tuhume guda huɗu na da alaƙa ne da zargin amfani da takardun karatu na bogi da bayar da bayanai na ƙarya akan hidimarsa ta ƙasa, yayin da sauran biyun kuma suka shafi karkatar da kuɗaɗe a lokacin da yake minista.

Saidai, tsohon ministan ya musanta baki ɗaya zarge-zarge guda shidda da aka gabatar da su akansa a kotun.

Masu gabatar da ƙarar sun shaida wa kotun cewa bincikensu ya gano hujar da ke nuna cewa Nnaji ya gabatar da takardun da ake da alamar tambaya akan sahihancinsu da kuma bayar da bayanan ƙarya akan takardun da ke ƙunshe da bayanan hidimarsa ga ƙasa.

Alƙalin kotun, Joyce Abdulmalik ta bayar da belin Nnaji akan Naira miliyan 20 bayan ya musanta zarge-zargen.

Haka kuma, ta umarce shi da ya miƙa fasfo ɗinsa na ƙasa-da-ƙasa, tare da hana shi fita daga Nijeriya ba tare da izinin kotu ba.

Daga nan ne ta ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 21 ga watan Yuli.

By Babaji

Leave a Reply