‘Yan bindiga sun sace shugaban makaranta a Oyo

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun yi awon-gaba da wani hedimasta mai suna Owoade Mathew Kolawale a garij Igbojaye da ke Ƙaramar Hukumar Itesiwaju ta jihar Oyo.

An gano cewa, ‘yan bindiga sun sace hedimastan mai kimanin shekaru 60 na makarantar Nomadic Basic School ne a yammacin ranar Asabar da tsakanin ƙarfe 5 zuwa 6.

A cewar ɗansa, Mista Owoade Abiola, an yi garkuwa da mahaifin nasa ne a lokacin da yake kan hanyar koma wa gida daga gona.

Majiyoyi sun ce jim-kaɗan bayan faruwar al’amarin, masu garkuwar sun kira iyalan dattijon ta wayarsa, inda suka nemi a biya Naira miliyan 30 a matsayin kuɗin fansarsa.

Blueprint.ng ta ruwaito cewa a safiyar ranar Lahadi, 12 ga Yuli, 2026 tawagar masu bincike ta gano babur ɗin hedimastan fake acikin juji.

Tuni dai iyalan nasa suka sanar da hukumomin tsaro halin da ake ciki domin su shiga tsakani wajen ganin an gaggauta ceto Mista Kolawale.

Hakan na zuwa ne kwanaki kaɗan da ceto ɗalibai da malaman Oriire da ke jihar su 40 daga hannun ‘yan bindiga bayan shafe kusan wata biyu a tsare.

By Babaji

Leave a Reply