Kogon Katsina, Hakimin Sabuwa a Jihar Katsina ya rasu

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Allah ya yi wa Hakimin Sabuwa kuma Kogon Katsina Injiniya Bello Ibrahim Kogo rasuwa.

Wata majiyar ta nuna cewa marigayi Bello Kogo ya rasu a wata asibiti da ke Kano bayan ya yi fama da rashi lafiya.

Babu wani ƙarin bayani sai ana sa ran gobe Talata za ayi jana’izar hakimin a gidan sa da ke garin Sabuwa a ƙaramar hukumar Sabuwa.

By ukarofi