Tinubu, Sarkin Musulmi, Sarkin Zazzau, Etsu Nupe, Ministan Labarai da wasu sun halarci taron tseren dawakai a Kaduna

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A ranar Asabar ne Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya jagoranci tawagar sarakunan gargajiya, manyan jami’an gwamnati da masu sha’awar wasan tseren doki a babban taron tseren dawakai na yammacin Afirka da aka gudanar a filin Murtala Muhammed da ke cikin garin Kaduna.

Gwamna Uba Sani na jihar ne ya wakilci Shugaban Ƙasar a taron karo na biyu, wato na Renewed Hope 2nd West Africa Horse Racing Derby.

Taron ya sami halartar Shehun Borno, Alhaji Abubakar Ibn Umar Garbai El-Kanemi, wanda ya wakilci Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III; Oluwo na Iwo, Oba Abdulrasheed Adewale Akanbi; da Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli.

Haka kuma, akwai Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris; tsohon gwamnan Kaduna, Mukhtar Ramalan Yero; Etsu na Nupe, Alhaji Yahaya Abubakar, da wasu sarakunan gargajiya da dama da jami’an gwamnati da kuma sauran manyan baƙi.

A jawabinsa a madadin Shugaba Tinubu, Gwamna Uba ya jaddada ƙoƙarin Gwamnatin Tarayya na amfani da wasanni a matsayin jarin inganta matasa, ciyar da tattalin arziƙi gaba da kuma samar da haɗin kan ‘yan ƙasa.

Haka kuma, ya taya Hukumar kula da lamuran Wasan Tseren Dawakai ta Tarayya murna bisa shirya irin taron a karo na biyu, yana mai bayyana wasan tseren dawakai a matsayin ɗaya daga cikin daɗaɗɗun wasannin gargajiya da aka fi so.

Kazalika, shugaba ƙasar ya yi jinjina ga marigayi Firimiyan Arewacin Nijeriya, Sir Ahmadu Bello, bisa kafa Hukumar Horar da Tsere ta Arewacin Nijeriya a shekarar 1962, matakin da a cewarsa, ya taimaka wajen haɗin kan ‘yan ƙasa da gina ta.

By Babaji

Leave a Reply