Zargin rashawa: Kotu ta bada belin tsohon shugaban Kotun Ɗa’ar Ma’aikata, Ɗanladi Umar kan miliyan N100

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Mai Shari’a Peter Kekemeke na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ya bayar da belin tsohon shugaban Kotun Ɗa’ar Ma’aikata (CCT), Ɗanladi Umar, wanda ke fuskantar gurfanarwa akan tuhume-tuhume guda huɗu na zargin saɓa wa dokokin aiki da rashawa.

Rahotanni sun bayyana cewa, Mai Shari’a Kekemeke ya ce an bada belin Ɗanladi Umar ne akan Naira miliyan 100 da kuma sharaɗin samo mutum ɗaya da zai tsaya masa da ke da shaidar mallakar wata kadara a Abuja.

Hakan na nufin tsohon shugaban na CCT zai cigaba da zama a kurkukun Kuje har sai an kammala cika sharuɗɗan belin.

A makon da ya gabata ne Alƙali Kekemeke ya umarci a tsare tsohon shugaban CCTn a gidan yarin Kuje har zuwa lokacin da zai shigar da buƙatar neman beli.

Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati EFCC ce ta gurfanar da Umar akan tuhume-tuhume guda huɗu da suka shafi cin mutuncin ofis a lokacin da yake jagorantar CCT.

By Babaji

Leave a Reply