El-Rufai yana tsare amma bai daina muzgunawa ba – Lukman bayyana dalilinsa na barin ADC

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Tsohon Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC na shiyyar Arewa maso Yamma, Salihu Mohammed Lukman, ya sanar da dakatar da kasancewarsa cikin ADC da kuma gamayyar jam’iyyun adawa, yana mai zargin wasu jagororin haɗakar da ci gaba da nuna masa ƙiyayya, musamman a Jihar Kaduna.

Rahotanni sun nuna cewa Lukman ya bayyana matakin ne a cikin wasiƙar da ya aike wa Shugaban ADC na ƙasa, Sanata Daɓid Mark, tare da kwafi ga wasu manyan jagororin gamayyar jam’iyyun adawa.

A cikin wasiƙar, ya bayyana cewa ya zama ba zai iya ci gaba da kasancewa cikin haɗakar ba sakamakon rikice-rikicen cikin gida da kuma saɓanin ra’ayi kan shugabanci da makomar gamayyar a Jihar Kaduna.

Lukman ya zargi tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, da wasu na kusa da shi da yi masa rashin adalci, yana mai cewa an tsara tsarin shugabancin haɗakar a jihar ne da gangan domin a ware shi daga harkokin tafiyar.

“Na san wannan mataki zai ba ka mamaki kuma Ina ba ka haƙuri. Amma gaskiya ba zan iya ci gaba da jure irin ƙiyayyar da wasu shugabannin Kaduna ke nuna min ba, musamman Malam Nasiru,” inji Lukman a cikin saƙonsa ga Sanata Daɓid Mark.

Ya ce bayan shafe sama da shekara guda yana ƙoƙarin sasanta ’yan adawa da gina haɗakar siyasa mai ƙarfi a Kaduna, sai ya tsinci kansa cikin abin da ya kira wani tsari na yaƙi da shi da El-Rufai da magoya bayansa suka jagoranta.

A cewarsa, abin ya sa ya ji kamar an yi watsi da shi a cikin ƙungiyar da ya taka muhimmiyar rawa wajen kafawa da bunƙasa ta, har ya ce an mayar da shi tamkar “baƙon da ba shi da gata” a cikin haɗakar da ya yi wa aiki tuƙuru.

“A wurin Malam Nasir da mutanensa, ni ne matsalar. Don haka na yanke shawarar cire musu wannan matsalar tare da sauran kowa,” inji shi.

Tsohon jigon APC ya ce dakatar da kasancewarsa cikin ADC da gamayyar jam’iyyun adawa wani mataki ne na kare mutuncinsa, yana mai cewa gara ya dakata daga siyasa na wani lokaci maimakon ya ci gaba da bin fata da ba za ta cika ba.

Lukman ya kuma nuna damuwa kan yadda wasu shugabannin haɗakar ke tafiyar da al’amura, yana mai zarginsu da rungumar irin salon siyasar da a baya suke suka lokacin da suke adawa da gwamnati.

Har ila yau, ya yi zargin cewa tsohon Gwamnan Jihar Ribas, Rotimi Amaechi, na hulɗa da wasu ’yan siyasa a Kaduna waɗanda bai gamsu da jajircewarsu wajen gina ADC ba, yayin da aka yi watsi da mutanen da suka sadaukar da lokaci da dukiyarsu wajen kafa tubalin jam’iyyar.

A cewarsa, wannan yanayi ya raunana amincewarsa da makomar gamayyar jam’iyyun adawa gabanin zaɓen 2027, yana mai gargaɗin cewa ADC na iya zama jam’iyya mai ƙaramin tasiri a fafatawar siyasar da ke tafe.

Sai dai Lukman ya jaddada cewa matakinsa ba ya nufin Shugaban ADC na ƙasa, Sanata Daɓid Mark, ko shugabancin jam’iyyar a matakin ƙasa, inda ya yabawa ƙoƙarinsu. Ya ce abin da ya sa ya dakatar da kasancewarsa cikin jam’iyyar shi ne irin yadda El-Rufai da wasu jiga-jigan haɗakar a Kaduna suka riƙa mu’amala da shi.

By ukarofi

Leave a Reply