Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano
Wasu masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa da yaɗa labarai a Kano sun bayyana ra’ayinsu na ganin an naɗa ɗan jarida kuma ma’aikacin Freedom Radio, Alhaji Salisu Baffayo, a matsayin Sakataren Yaɗa Labaran Mataimakin Gwamnan Kano, Alhaji Murtala Sule Garo.
Masu wannan ra’ayi sun ce Salisu Baffayo na da ƙwarewa da gogewa a aikin jarida tare da kyakkyawar alaƙar aiki da Murtala Sule Garo, lamarin da zai taimaka wajen gudanar da aikin cikin nasara.
Sun kuma bayyana cewa ƙwarewarsa da saninsa a fagen sadarwa da hulɗa da jama’a za su kasance ƙarin tagomashi ga ofishin mataimakin gwamnan.
Sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto babu wata sanarwa a hukumance daga ofishin mataimakin gwamnan dangane da naɗin mai magana da yawunsa.
Masu wannan ra’ayi sun bayyana fatansu na ganin an yi la’akari da ƙwarewa da gogewa wajen duk wani naɗi da za a yi a nan gaba.
