
Ƙungiyar ‘Yan kasuwa Masu Gidajen Mai ta Ƙasa (IPMAN) ta ce rashin tabbas da ake fuskanta kan farashin fetur ya sa wasu daga cikin mambobinta dakatar da sake sayen mai, lamarin da ya haddasa rufe wasu gidajen mai na ɗan lokaci.
Shugaban IPMAN na shiyyar Yamma, Chief Oyewole Akanni, ne ya bayyana hakan yayin wata hira da Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) a Ibadan ranar Lahadi.
Akanni ya ce sauye-sauyen farashin fetur da ake samu akai-akai sun sanya masu gidajen mai cikin yanayi na rashin tabbas, domin suna fargabar sayen fetur da farashi mai tsada sannan daga baya farashin ya ragu kafin su sayar, abin da kan jawo musu asara.
Ya ce saboda haka ne da dama daga cikin masu gidajen mai suka dakatar da yin sababbin odar fetur har sai kasuwa ta samu kwanciyar hankali.
A cewarsa, matakin ya sa wasu gidajen mai suka rufe na ɗan lokaci saboda rashin isasshen man fetur da za su sayar.
Shugaban na IPMAN ya yi kira ga gwamnatin tarayya da sauran masu ruwa da tsaki a ɓangaren man fetur da su samar da tsarin farashi mai ɗorewa da zai rage rashin tabbas a kasuwa tare da kare masu zuba jari daga asara.
Ya kuma yi gargaɗin cewa idan aka ci gaba da samun sauye-sauyen farashi ba tare da samun daidaito ba, hakan na iya ƙara shafar wadatar fetur da kuma harkokin kasuwancin masu gidajen mai a faɗin Nijeriya.
