Sharhin littafin ‘Sanin Asali Shine Farin Cikin Rayuwa Da Aminci’

Spread the love

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU 

Sunan littafi: Sanin Asali Shine Farin Cikin Rayuwa Da Aminci

Mawallafi: Sheikh Abdulƙadir Na’Annabi Mu’azu

Shekarar bugawa: 2026

Yawan shafi: 80

Mai sharhi: Abba Abubakar Yakubu

Wane ne Sheikh Na’Annabi Mu’azu?

Sheikh Abdulƙadir Na’Annabi Mu’azu wani fitaccen malamin addinin Musulunci ne da ke zaune a Jos, Jihar Filato. Allah Ya yi wa wannan malami baiwar sanin ilimin luggar Larabci da Balagha. Sannan malamin gwani ne wajen rubuta waƙoƙin Larabci da na Hausa, masu ƙunshe da darussa iri-iri. Ya kuma rubuta wasan kwaikwayo na Larabci da suka shafi tarihin Musulunci, da wasu fitattun malaman Musulunci. Sanin Asali Shine Farin Cikin Rayuwa Da Aminci, shi ne littafinsa na 7 da ya samu damar wallafawa, yayin da yanzu haka a ƙasa akwai wasu kimanin 40 da bai samu damar bugawa ba. Sheikh Na’Annabi, kamar yadda aka fi saninsa shi ne shugaban ɗariƙar ƙadiriyya na Jihar Filato. Mamba ne a Majalisar Malaman Musulunci dake ƙarƙashin Jama’atu Nasril Islam ta Jihar Filato. Yana zaune ne a gidan ƙadiriyya dake Layin ‘Yandoka a cikin garin Jos. 

Wanne saƙo littafin ke isarwa?

An rubuta littafin ne a matsayin tunatarwa da faɗakarwa game da muhimmancin zumunci a tsakanin ƴan’uwa na jini. Malamin ya rubuta littafin ne domin taskace tarihi da kuma samar da wani kundi na gano salsala da dangantaka tsakanin ƴan’uwa na wannan zuriya ta Audun Amo da ta samo asali daga Maroko (Maghrib) zuwa Tudun Nufawa a cikin Jihar Kano. 

Shaihun malamin ya buga wannan littafi ‘Sanin Asali Shine Farin Cikin Rayuwa Da Aminci’ cikin harshen Hausa ne, domin bai wa ƴan’uwa da aka yi littafin saboda su, da kuma sauran jama’a da littafin zai samu damar shiga hannunsu, sauƙin karantawa da fahimtar saƙon da ke ciki, ba lallai sai ɗalibin adabin Larabci ba.

A tsakanin shafuka 80, Sheikh Na’Annabi Mu’azu, kasafta littafin zuwa babi-babi, inda ya raba shi zuwa gida 4, inda a ciki ya yi bayani kan tarihi, salsala, da kuma zuriyar kowanne daga kan kakanni da iyaye, zuwa jikoki. Har ya kai ga danganta da tsatson Shaihu Atiku ɗan Shaihu Usmanu ɗanfodiyo, sakamakon hijira da auratayya da aka riƙa samu tsawon shekaru.

Daga cikin tarihin da malamin ya bayar ya taɓo yadda zuri’ar sa ta haɗu da wannan babbar zuri’a mai albarka ta Audun Amo, wacce ya dangantata da Sheikh Abdulrahman da ake yi wa laƙabi da Wali Cigero. Haka kuma ya taɓo tarihin yadda mahaifinsa, Malam Mu’azu Mai Bandiri, ya baro Birnin Kano zuwa Jos, bisa umarnin malaminsa kuma shehinsa, Amirul Jaishi Sheikh Muhammadu Nasiru Kabara, domin yaɗa ɗariƙar ƙadiriyya.

A ƙarshen littafin malamin ya yi bayani kan hanyoyin da ya bi wajen tattara bayanan da ya rubuta, domin taskace su a cikin littafi guda, wanda suka shafi abin da ake ce wa, kunne ya girmi kaka. ɗaya daga cikin hanyoyin da masana ilimin tarihi suka amince a kai wajen tattara bayanai na bincike, kai tsaye daga waɗanda abin ya shafa ko suka yi rayuwa da waɗanda tarihin ke magana a kansu. Don haka malamin ya yi tattaunawa ta baki da baki da wasu daga cikin magabata maza da mata, da suka haɗa har da mahaifinsa, Marigayi Malam Mu’azu Mai Bandiri.

Wannan littafi tasirinsa da muhimmancinsa na da yawa sosai, ba ga ƴan’uwa da danginsa kaɗai ba har da sauran jama’a, ɗalibai, da manazarta ilimin tarihi. Saboda malamin ya yi wa littafin tsarin yadda matasa masu tasowa za su amfana da ilimin da ke ciki sosai, ba tare da sai an yi musu fashin baƙi ba. An yi amfani da lissafin shekarar Miladiyya, da kwatance na masana ilimin taswira wajen bayyana nisa da girman waje. Mun ga yadda malamin ya ɗauko tarihin ƙasar Maghrib, wacce take a Arewa maso Yamma a nahiyar Afirka da ta yi iyaka da Baharul Mutawassil wato tekun Meditarenian, ta Arewa da kuma ƙasar Aljeriya ta ɓangaren Kudu. Don haka, wannan littafi ba tarihi ne kawai na wata zuri’a ba, tarihi ne na wata al’umma da ta rayu a yammacin Afirka, ta yaɗu a sassan Arewacin Nijeriya, ta kuma amfanar da jama’a da dama, musamman wajen yaɗa ilimin addinin Musulunci, kasuwanci, da zaman lafiya.

Kurakurai:

Duk wani abu da ya cika da kyau da kamala, ba za ka rasa shi da wata tawaya ko yaya take ba. Don haka samun wasu kurakurai a littafin ba yana nufin naƙasu ba ne ga marubucin ko waɗanda suka yi hidima a kansa, amma ƙarin ƙwarin gwiwa ne, don a kiyaye gaba. Kamar yadda masana ilimin talifi ke faɗa ne, babu wani littafi cikakke kuma kammalalle da babu kuskure ko kaɗan a cikinsa, idan ba Alƙur’ani Mai Girma ba, musamman a wajen mu Musulmi. Abin da ake buƙata idan manazarta sun yi irin wannan tsokacin to, a samu wani ko wasu da za su ɗora nasu binciken a kai. Ko kuma shi marubucin ya yi gyara a lokacin da ya tashi sake yin bugu na biyu.

1. Nazari game da sunan littafin

A ganina, kuma a matsayina na almajiri, ina ganin Malam Na’Annabi ya yi amfani da ƙwarewarsa a fagen rubutun littattafan Larabci ne ya sa ya zaɓi amfani da kalmomi masu yawa wajen sanya sunan littafin. ‘Sanin Asali Shine Farin Cikin Rayuwa Da Aminci’, ina ganin ya yi tsayi sosai a matsayin littafin tarihi na Hausa. Za a iya taƙaita kalmomin zuwa kalmomin da ba su wuce 4 ko 5 ba, a maimakon 10 da aka yi amfani da su. 

2. ƙa’idojin rubutu 

An samu kurakurai sosai wajen kiyaye ƙa’idojin rubutun Hausa. Na lura kamar wanda ya taimaka wa Malam wajen hidimar rubutun bai ƙware sosai wajen sanin ƙa’idojin rubutun Hausa ba. Sannan an rubuta wasu kalmomin da Turanci maimakon Hausa. An haɗe wasu kalmomi a maimakon a raba su, an raba a inda ya kamata a haɗa. Wannan zai bai wa mai karatu wahala wajen fahimtar me marubucin ke nufi a wani wajen. Don haka, idan an samu dama ya kamata a gyara.

3. Yadda aka saka abubuwan da ke ciki

Na lura a kowanne babi cikin babi 4 da aka yi cikin littafin, an yi masa tsarin mabudin littafin a inda ake rubuta ABUBUWAN DA KE CIKI, wato Table of Content, nasa daban; a maimakon a haɗe su a farkon littafin, wanda hakan ya saɓa wa yadda ake aikin buga littafi.

4. Salsalar malam Na’Annabi a ɓangaren uwa da uba

A kashin farko na littafin, Malam Na’Annabi ya kawo salsalar mahaifinsa a shafi na 17 da yadda dangantakar sa ta kai ga Wali Cigero. Amma na lura ya tsallake kawo ƴaƴan Malam Mu’azu Mai Bandiri, kamar yadda ya yi akan sauran ƴan dangin da ya kawo tarihin su daki-daki. Sai ya jinkirta kawo su sai a can kusa da ƙarshen littafin a shafi na 73 ya kawo sunayen ƴan’uwansa a lokacin da yake bayani kan tushen mahaifiyarsa Baaba Rakiya wacce dangantakarta ta kai ga Shaihu Usmanu ɗanfodiyo ta tsatson ɗansa Shaihu Atiku.

A ganina, zai yi kyau a ce a dukkan ɓangarorin an kawo silar da kuma adadin ƴaƴan mahaifinsu, saboda wani lokaci mai karatu yana iya datsar karatunsa daga wani shafi daban, a maimakon daga bango zuwa bango. Musamman kuma almajiran malamin da masoyansa da za su so karanta salsalar malamin za su so su ga sunan malamin da dangantakar mahaifinsa a kashin farko na littafin.

Shawarwari

1. Zai yi kyau nan gaba idan za a sake aikin wannan littafin a sanya hotuna, na wasu wurare, gine-gine, da tsofaffin magabata, domin masu tasowa su ga fuskokin kakaninsu, da wuraren da iyaye da kakaninsu suka zauna. Wannan shi ne tsarin da akasari littattafan tarihi ke amfani da shi.

2. Zai yi kyau a samar da Babi Na Biyar, wanda zai yi bayani kan irin baiwar da Ubangiji Allah Ya albarkaci wannan zuri’a da ita, domin ƙara yabawa da albarkarSa gare su.

Ina fatan sauran jama’a ma za su kwaikwayi marubucin wajen gudanar da bincike game da tarihin asalin zuri’ar su da taskace shi a littafi, domin sauran zuri’a da masu tasowa ‘yan baya su koya. Yanzu dai Malam  ya buɗe mana ƙofa!

Allah Ya ƙara wa Malam lafiya da nisan kwana, kuma albarkaci zuri’ar sa da mu bakiɗaya. Allah Ya saka wa duk waɗanda suka taimaka wajen ganin wannan littafi ya isa ga jama’a, daga rubutunsa, har shigar da shi na’urar kwamfiyuta da buga shi. 

Alhamdulillah.

By ukarofi

Leave a Reply