Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a katsina
Kwamishinan ilimi a Jihar Katsina Alhaji Yusuf Suleiman Jibiya ya bayyana cewa daga yanzu darussan da malamai na makaratun firamare da sakandire za su koyar zai daidaita da irin karatun da su ka yi.
Haka kuma gwamnatin Katsina za ta rinƙa tura su aikin malanta a mahaifar su.
Kwamishinan wanda ke magana da manema labarai a ofishin sa ya sanar da cewa gwamna Dikko Raɗɗa ya amince da biyan Naira dubu 30 a matsayin alawus ga malamin da ke koyar wa a karkara da kuma basu rancen buburan hawa mai amfani da hasken rana a matsayin rance da za su biya bisa rangwame.
Alhaji Yusuf Suleiman ya ce duk wannan matakai da gwamnatin Katsina ta ɗauka ta yi ne domin ba malaman ƙwarin gwiwan zama a ƙauyukan su domin kaucewa rashin zuwa da makara a wajen aiki.
Ya sanar da cewa malamai 2158 da gwamnati ta ɗauka aiki a kwanan baya sun faɗo cikin wannan tsari inda kowanne zai karantar a yankin da yake zama.
Duk dai a ƙoƙarin gwamnatin Dikko Raɗɗa na inganta Ilimi a Jihar, gwamnati tana gina ƙarin makaratun sakandire guda 30 a faɗin jihar wanda ana gab da kammala aikin gina makaratun.
A yankin da ake fama da rashin tsaro, kwamishinan ya tabbatar da cewa mafi yawan makarantun firamare da sakandire sun buɗe sakamakon zaman lafiya da ya inganta sai irin ɗan abinda ba a rasa ba.
Kwamishinan ya tabbatar da cewa gwamnatin ta buɗe kusan duk makarantun da suka daɗe suna rufe sakamakon rashin tsaro.
Ya ce suna jiran shugabannin al’ummar yankin da makarantun a rufe da su rubutawa gwamnati da buƙatar buɗewa,”sai gwamnati ta tabbatar da ingantar tsaro ɗari bisa ɗari kan ta buɗe wata makaranta,”Inji Suleiman.
Yanzu haka a cewar kwamishinan an kusa kammala aikin gina ƙarin makaratun sakandire guda 30 kuma da zaran an kammala za a ƙara gina wasu Junior Secondary School guda 44 a faɗin jihar.
Kwamishinan ya yaba wa gwamna Dikko Raɗɗa a ƙoƙarin sa na ba harkar Ilimi fifiko ta hanyar ɗaukar ƙwararrun malamai da samar da kayayyakin koyarwa a makaratun Jihar.
